Zargin Ta’addanci: Buratai Ya Maka Tsohon Soja a Kotu, Ya Nemi Diyyar N1bn

Zargin Ta’addanci: Buratai Ya Maka Tsohon Soja a Kotu, Ya Nemi Diyyar N1bn

  • Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya kai kara kotu bayan zarginsa da hannu a ta'addanci
  • Buratai ya kai ƙarar bayan bata suna inda ya bukaci makudan kudi kan bata suna daga Mango-Janar Danjuma Ali-Keffi mai ritaya
  • Ya buƙaci kotu ta tilasta janye kalaman, neman afuwar jama’a, tare da hana Ali-Keffi sake maimaita irin waɗannan zarge-zarge

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar-Janar Tukur Yusufu Buratai (mai ritaya), ya kai kara kotu kan bata masa suna.

Buratai ya shigar da ƙarar kan bata suna ta Naira biliyan ɗaya a kan wani tsohon babban jami’in soja, Manjo-Janar Danjuma Hamisu Ali-Keffi (mai ritaya).

Buratai ya shiga kotu da tsohon soja kan zarginsa da ta'addanci
Tsohon hafsan sojoji, Tukur Buratai a Abuja. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Yaushe Tukur Buratai ya shigar da karar?

Tsohon hafsan sojojin ya shigar da korafin ne a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sunan Matawalle ya fito a zargin cafke hadimin Gwamna Dauda, APC ta yi magana

An shigar da ƙarar ne a ranar 8 ga Janairu, 2026, a sashen shari’a na Kaduna, inda Buratai ya zargi Ali-Keffi da yaɗa kalamai ƙarya da ɓata suna, waɗanda ke alaƙanta shi da ɗaukar nauyin ta’addanci.

Ta bakin lauyoyinsa, A.I. Aliyu da A.M. Hassan, Buratai ya buƙaci kotu ta bayyana kalaman da ake dangantawa da wanda ake ƙara a masayin kalamai ne na bata suna da suka lalata mutuncinsa.

Daga cikin kafafen da aka wallafa har da Sahara Reporters da sauran kafafen labarai da na sada zumunta.

Takardun kotu sun nuna cewa Buratai ya ce Ali-Keffi ya yi hira da wasu kafafen labarai a shekarar 2025, inda ya nuna alamar cewa Buratai na da alaƙa da ‘yan ta’adda da masu ɗaukar nauyin ta’addanci, tare da zargin cewa ya shiga wata makarkashiya ta ɓoye ayyukan ta’addanci a lokacin da yake Babban Hafsan Sojin Ƙasa.

Buratai ya kadu da aka alakanta shi da ta'addanci
Tsohon hafsan sojoji a Najeriya, Tukur Buratai. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Buratai ya caccaki Ali-Keffi kan zargin ta'addanci

Buratai ya kuma zargi Ali-Keffi da rashin hankali, duk da cewa a cikin wasu wallafe-wallafen, shi ma Ali-Keffi ya amince cewa babu wani bincike da ya tabbatar da alaƙarsa da ɗaukar nauyin ta’addanci.

Saboda haka, Buratai ya roƙi kotu ta umurci Ali-Keffi da ya janye kalaman nan take, tare da buga neman afuwar jama’a ba tare da wani sharadi ba, a Sahara Reporters, jaridun ƙasa guda biyu, da kuma dukkan kafafen sada zumunta da aka yaɗa kalaman.

Kara karanta wannan

Tsohon hafsan sojoji ya nausa kotu kan zargin yana da alaka da ta'addanci

Har ila yau, Buratai na neman diyyar ₦1bn a matsayin diyya ta gaba ɗaya kan bata suna, la’akari da tsananin zargin ta’addanci, cewar rahoton Vanguard.

Takardar sammaci ta umurci Ali-Keffi da ya bayyana a gaban kotu cikin kwanaki 21 inda kotu za ta iya sauraron shari’ar ko da bai halarta ba idan ya gaza yin hakan.

Zargin ta'addanci: Tsohon hafsan sojoji ya je kotu

An ji cewa tsohon Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya (mai ritaya), ya garzaya kotu kan zargin da ke danganta shi da ta’addanci.

Yahaya ya bai wa wadanda suka yi zargin da kafafen yada labarai wa’adin awanni 72 su janye kalamansu tare da neman afuwa.

Tsohon sojan ya ce matakin shari’ar na da nufin kare mutuncinsa da kuma tsare gaskiya da kwarewa a hukumomin tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.