NLC Ta Yi wa Tinubu Barazana saboda a Dakatar da Dokokin Haraji
- Kungiyar kwadago ta NLC ta sake gargadin gwamnatin tarayya kan aiwatar da sababbin dokokin haraji, tana mai cewa hakan kara nauyi ne kan talakawa
- Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce an tsara dokokin ba tare da tuntubar ma’aikata ba duk da cewa su ne manyan masu biyan haraji a Najeriya
- Tsofaffin shugabannin kwadago da manyan ‘yan siyasa sun bayyana ra'ayoyi kan yadda ya dace a tunkari manufofin da ake ganin ba daidai suke ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta dakatar da aiwatar da sababbin dokokin haraji tana mai gargadin cewa watsi da bukatunta na iya jawo fuskantar kalubale babba.
Wannan gargadi ya fito ne daga bakin Shugaban NLC, Joe Ajaero, a yayin wani taro da aka gudanar a Abuja domin kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban NLC, Hassan Summonu, a bikin cikar sa shekaru 85 a duniya.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa Ajaero ya ce tsarin harajin da aka bullo da shi ya zo ne a lokacin da ‘yan kasa ke fama da matsin tattalin arziki, lamarin da ya kara tada hankalin ma’aikata da kungiyoyin kwadago.
Ƙungiyar NLC ta soki dokokin harajin Tinubu
Joe Ajaero ya bayyana cewa an tsara dokokin harajin ne ba tare da shigar da ra’ayoyin ma’aikata daga bangaren gwamnati da masu zaman kansu ba, duk da kasancewarsu manyan masu biyan haraji a kasar.
Ya ce tun daga kwamitin shugaban kasa kan gyaran haraji har zuwa matakin majalisa, an yi watsi da ra’ayoyin ma’aikata gaba daya, lamarin da ya haifar da dokoki da ke kara tsananta rayuwar talakawa.
A cewarsa, duk wani haraji da ke shafar mutanen da ke rayuwa cikin tsananin talauci ba za a iya kiran sa adalci ko ci gaba ba, domin yana kara gibin da ke tsakanin masu hali da marasa shi.
NLC ta yi barazanar daukar mataki
Shugaban NLC ya bukaci gwamnati da ta dakatar da aiwatar da dokokin, ta sake duba su tare da gyara tsarin yadda zai dace da halin da jama’a ke ciki.
The Guardian ta rahoto cewa ya jaddada cewa ya kamata dokoki masu inganci su karfafa hukumomi da tsarin kasa, ba su raunana su ba.
Ajaero ya yi nuni da cewa idan aka ci gaba da watsi da bukatun ma’aikata, kungiyar kwadago ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakan da suka dace domin kare su.
Ra’ayoyin Oshiomhole da Obasanjo
A nasa jawabin, Sanatan da ke wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya bukaci shugabannin kwadago da su tashi tsaye su kalubalanci duk wata manufa da suke ganin ba ta adalci.
Ya ce korafi kadai ba zai warware matsalolin ma’aikata ba, yana mai cewa idan kungiyoyin kwadago suka ci gaba da gunaguni ba tare da daukar mataki ba, ba za a saurare su ba
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa gyaran da ya yi wa kungiyar kwadago a lokacin mulkinsa ya samo asali ne daga bukatar tabbatar da ‘yancin kai da ikon kasa.

Source: Getty Images
Ya ce duk da cewa ba kwararre ba ne a harkar kwadago, burinsa shi ne ganin an gina kungiya mai zaman kanta da ke aiki domin muradun kasa baki daya.
Legit ta tattauna da ma'aikaci
Wani ma'aikaci da ya tattauna da Legit Hausa ya bayyana cewa duk wata ana cire musu haraji saboda haka yana da kyau a ba su muhimmanci wajen yin dokar.
Duk da haka, Malam Hamza Abu Abdullahi ya nuna shakku kan tasirin makatin da NLC za ta dauka:
"Bai wuce NLC ta tafi yajin aiki ba ne idan aka ki sauraronta. Kuma mun ga yadda aka yi irin haka a baya ba tare da samun wata nasara ba."
NLC ta nemi karin albashi ga ma'aikata
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kwadago na kasa, Joe Ajaero ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta shirya karawa ma'aikata albashi.
Legit Hausa ta rahoto cewa Joe Ajaero ya bayyana haka ne a sakon barka da shiga sabuwar shekara da ya fitar bayan shiga 2026.
Shugaban NLC ya ce tsadar kayayyaki da ake ciki ya sanya karin mafi karancin albashi da aka yi zuwa N70,000 ba shi da wata fa'ida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


