Sojoji Sun Raraka 'Yan Fashi da Suka Tare Jama'a a Hanyar Kaduna zuwa Abuja

Sojoji Sun Raraka 'Yan Fashi da Suka Tare Jama'a a Hanyar Kaduna zuwa Abuja

  • Sojojin Najeriya sun dakile harin fashi da makami a babbar hanyar Abuja–Kaduna ba tare da asarar ran matafiya ko sojoji ba
  • Rundunar ta ceto matafiya tare da kama wani daga cikin ’yan fashin bayan an yi gumurzu a lokacin da aka samu labarin harin
  • Tuni aka samu damar dawo da zaman lafiya yankin bayan an kwashe matafiyan da yan fashin suka rutsa a hanya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Rundunar sojojin Najeriya a ƙarƙashin Operation fansan yamma ta samu nasarar dakile wani harin fashi da makami a kan babbar hanyar Abuja–Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata, 6 ga Janairu, 2026, lokacin da sojojin ke kan sintiri na yau da kullum, suka samu kiran gaggawa game da wani harin fashi da makami a yankin Nasarawan Doka.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe wani uban daba a Kano da rikici ya barke tsakanin kungiyoyi 2

Sojojin Najeriya sun dakile harin 'yan fashi
Wasu daga cikin sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa bayan samun bayanan, sojojin sun gaggauta matsawa zuwa wurin ba tare da ɓata lokaci ba.

An yi artabu tsakanin sojoji da 'yan fashi

TVC News ta wallafa cewa sojojin sun yi artabu da ’yan fashin, suka kuma dakile barazanar da matafiyan suka fuskanta.

Wannan na cikin sanarwar da Laftanar Kanal Shuaib Umar, mukaddashin mataimakin darektan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Nijeriya, Sashen na 1 na 'operation' fansan yamma ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta bayyana cewa sojojin sun yi gaggawar daukar mataki ne domin kare jama’a, kuma sun yi nasarar tarwatsa harin gaba ɗaya.

Sojoji sun kama 'dan fashi

A yayin artabun, an kama wani daga cikin ’yan fashin mai suna Kabiru Zayyanu, wanda ya samu raunin harbin bindiga a ƙafarsa.

An kama dan fashi a titin Abuja zuwa Kaduna
Taswirar jihar Kaduna, inda aka fafata tsakanin 'yan fashi da sojoji Hoto: Legit.ng
Source: Original

An gaggauta kai shi asibitin a jihar Kaduna, inda aka ba shi agajin gaggawa. Sauran ’yan fashin sun tsere daga wurin bayan sun ji zafin wuta.

Kara karanta wannan

Borno: Sojoji sun taka bama bamai a hanyar kai wa ƴan ta'adda farmaki, an yi asarar rayuka

Sojojin sun bi sawun ’yan fashin da suka tsere domin ci gaba da binsu, amma sun tsere ba a samu damar cimma masu ba.

Duk da haka, hukumar ta tabbatar da cewa babu wani mutum da ya rasa ransa ko aka sace a yayin wannan harin.

Sanarwar ta ƙara da cewa bayan kammala bincike, za a miƙa wanda aka kama ga hukumomin tsaro da suka dace domin ci gaba da shari’a.

Haka kuma, an bayyana cewa halin tsaro a yankin ya kasance cikin kwanciyar hankali, yayin da sojoji ke ci gaba da mamaye yankin da tabbatar da tsaro mai ƙarfi.

Rundunar Sojin Najeriya ta sake jaddada aniyarta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da kira ga ’yan ƙasa da su rika ba wa hukumomin tsaro bayanai.

Za a dauki karin sojoji aiki

A wani labarin, mun wallafa cewa rundunar sojin Najeriya ta bayyana sabuwar aniya ta ɗaukar sababbin sojoji 24,000 domin ƙara ƙarfin aikinta da kuma inganta yaƙi da ta'addanci.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shuaibu, yayin wata ziyarar aiki da ya kai Jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

'Mutane sun fara guduwa,' Halin da ake ciki a Neja bayan kashe fiye da mutum 40

A cewar Shugaban rundunar, buƙatar ƙarin sojoji ta zama dole ne sakamakon faɗin yankunan da rundunar ke da alhakin karewa da fuskantar matsalolin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng