Duk da Janye Korafin Dangote, ICPC Ta Taso Tsohon Shugaban NMDPR a Gaba

Duk da Janye Korafin Dangote, ICPC Ta Taso Tsohon Shugaban NMDPR a Gaba

  • Hukumar ICPC ta bayyana cewa ba za ta dakatar da binciken cin hanci da ake yi wa Ahmed Farouk ba duk da janyewar korafin Aliko Dangote
  • Fitaccen dan kasuwa, Aliko Dangote ya janye koken da ya shigar, amma ICPC ta ce doka ta ba ta ikon ci gaba da bincike
  • Zargin ya shafi almundahana, cin hanci da kashe kuɗin gwamnati ba bisa ka’ida ba da sauran zarge-zarge da suka tada kura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Hukumar yaki da cin hanci da sauran manyan laifuffka ta 'kasa (ICPC) ta bayyana cewa za ta ci gaba da binciken tsohon Shugaban hukumar NMDPR.

Kara karanta wannan

Nijar da kasashe 2 sun ci bashin wutar lantarkin N25bn a Najeriya sun gaza biya

Hukumar ta ce tana bibiyar zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon Shugaban, Ahmed Farouk, duk da janyewar koken da Alhaji Aliko Dangote ya shigar.

ICPC ta ce ana ci gaba da binciken Ahmed Farouk
Tsohon Shugaban hukumar NMDPRA, Ahmed Farouk Hoto: @ImranMuhdz
Source: Twitter

Thisday ta wallafa cewa hukumar ta tunatar da jama’a cewa Ahmed Farouk ya yi murabus daga shugabancin NMDPRA jim kaɗan bayan Dangote ya shigar da koke a gaban ICPC.

Koken Dangote kan tsohon Shugaban NMDPR

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Dangote ya nemi a kama Ahmed Farouk tare da gudanar da bincike kan zargin cin hanci.

Sai dai kafin hukumar ta kammala binciken, Dangote ya aike da wasiƙa yana roƙon a dakatar da binciken domin ya janye.

Amma a wata sanarwa da kakakin ICPC kuma Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, John Odey, ya fitar, ya ce bincike fa babu fashi.

Ya kara da cewa duk da karɓar wasiƙar janye koke mai dauke da kwanan wata 5 ga Janairu, 2025, daga Dr. O.J. Onoja, SAN, lauyan Dangote, ICPC ba za ta dakatar da binciken ba.

Kara karanta wannan

Dangote ya aika wasika ga ICPC, ya canza shawara kan korafin da ya shigar da Farouk Ahmed

ICPC na ci gaba da binciken Ahmed Farouk

Hukumar ta jaddada cewa bisa sashe na 3(14) da 27(3) na dokar kafuwarta, binciken da aka riga aka fara domin kare muradun jama’ar Najeriya zai ci gaba ba tare da tsaiko ba.

A cikin koken da Dangote ya shigar a ofishin Shugaban ICPC, Musa Aliyu (SAN), ya zargi Ahmed Farouk da kashe sama da $7m wajen biyan kuɗin karatun ’ya’yansa huɗu a ƙasar Switzerland.

Alhaji Aliko Dangote ya janye korafin da ya shigar kan Ahmed Farouk
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote Hoto: Bloomberg
Source: Getty Images

Dangote ya ƙara da cewa Farouk ya yi amfani da matsayinsa na Shugaban NMDPRA wajen cin zarafin ofis, inda ya karkatar da kuɗin gwamnati domin amfanin kansa.

Ya bayyana cewa waɗannan ayyuka sun saba wa ƙa’idar ɗabi’a ga ma’aikatan gwamnati, tare da haddasa fushin jama’a da zanga-zanga daga wasu ƙungiyoyi.

Dangote ya aika wasika ga ICPC

A wani labari, mun wallafa cewa Alhaji Aliko Dangote ya aika wasika ga hukumar yaki da cin hanci da manyan laifuffuka a kasar nan kan korafin da ya shigar kan Ahmed Farouk.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Kotu ta kwace kadarori 57 na Malami a Kano, Abuja da wasu jihohi 2

Lauyan Dangote ne ya tabbatar da janye korafin a wata wasika da ya aika wa ICPC mai dauke da kwanan watan 5 ga watan Janairu, 2025 a madadin hamshakin attajirin.

Tun farko, rikici ya shiga tsakanin Dangote da Injiniya Farouk Ahmed ne kan zargin rashin gaskiya da taba dukiyar gwamnati da yake ofis, har ta kai Farouk Ahmed ya bar kujerarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng