An 'Sace' Wani Hadimin Gwamnan Zamfara, Ana Zargin Akwai Sa Hannun Nuhu Ribadu

An 'Sace' Wani Hadimin Gwamnan Zamfara, Ana Zargin Akwai Sa Hannun Nuhu Ribadu

  • Gwamnatin Zamfara ta nemi Shugaba Bola Tinubu ya sa baki a sako Saleem Abubakar wanda aka ce jami'an tsaro sun 'sace' a Abuja
  • Mai magana da yawun Gwamna Dauda Lawal ya yi ikirarin cewa daga ofishin Nuhu Ribadu ne aka tura jami'an tsaro suka sace Saleem
  • Amnesty International ta bayyana kamun a matsayin haramtacce sannan ta yi kira ga gwamnati da ta daina musgunawa 'yan adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sa baki kan abin da ta kira "garkuwa" da Saleem Abubakar, wani hadimin Gwamna Dauda Lawal, wanda aka kama a Abuja.

Kiran na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sulaiman Idris, mai magana da yawun gwamnan ya fitar a ranar Talata, 6 ga Janairu, 2026, a Gusau, kuma aka rabawa manema labarai.

Kara karanta wannan

Matakin da gwamnati ta ɗauka bayan ƴan ta'adda sun kashe fiye da mutum 30 a Neja

Gwamnatin Zamfara ta zargi ofishin Nuhu Ribadu da tura jami'an tsaro suka 'sace' hadimin gwamna a Abuja.
NSA, Nuhu Ribadu (hagu), Saleem Abubakar (tsakiya) da gwamnan Zamfara, Dauda Lawal (dama). Hoto: @AmnestyNigeria, @daudalawal_, @NuhuRibadu
Source: Twitter

An 'sace' hadimin gwamnan Zamfara

A cikin sanarwar, gwamnatin Zamfara ta zargi dakarun tsaro na musamman daga ofishin mai bayar da shawara kan tsaron ƙasa (NSA) da sace Saleem Abubakar ba tare da wani sammacin kotu ba, in ji rahoton The Cable.

Gwamnatin jihar ta yi zargin cewa Ministan tsaro, Bello Matawalle, ne ya kitsa wannan kamun ta hanyar amfani da ofishin Nuhu Ribadu domin tsoratar da ’yan adawa.

Idris ya bayyana cewa an kai Saleem wani wurin da ba a sani ba, sannan daga baya aka sake samun bayanai cewa an sauya masa wurin da aka tsare shi domin ɓatar da sawu.

Gwamnati ta nemi shugaban ƙasa da ya tsawatar wa ofishin Nuhu Ribadu, tana mai cewa idan har akwai wani laifi da ake zargin Saleem ya aikata, to ya kamata a kai shi kotu maimakon ɓatar da shi.

Amnesty International ta yi Allah-wadai

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon kwamishinan ilimi ya rasu yana da shekaru 78 a jihar Kaduna

A ɓangare guda, ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta duniya, Amnesty International, ta yi Allah-wadai da abin da ta kira kamun zalunci da aka yi wa Saleem Abubakar (wanda aka fi sani da Salim Musa).

A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a ranar Laraba, kungiyar ta bayyana cewa jami’an ’yan sanda ne suka bibiyi Saleem har zuwa wani otel da ke unguwar Apo a Abuja.

Amnesty International, ta yi ikirarin cewa jami'an tsaron da suka kutsa otel din ɗauke da makamai sun yi awon gaba da Saleem.

Gwamnatin Dauda Lawal ta roki Tinubu ya sa baki bayan an kama wani hadimin gwamna
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya na jawabi a ofishinsa da ke gidan gwamnati, Gusau. Hoto: @daudalawal_/X
Source: Facebook

Mene ne dalilin kama hadimin gwamnan Zamfara?

Amnesty ta ce an tsare Saleem ne a sanannen wurin nan na "Abbatoir" da ke Abuja sakamakon amfani da shafukan sada zumunta wajen sukar wasu jami’an gwamnati.

Ƙungiyar ta gargaɗi gwamnati kan ƙoƙarin murƙushe muryoyin matasa da ke bayyana ra’ayoyinsu, tana mai jaddada cewa sukar jami’an gwamnati ba laifi ba ne.

Ta kuma koka kan yadda ’yan sanda suka musanta cewa Saleem yana hannunsu lokacin da lauyoyinsa da danginsa suka je nemansa.

An bukaci Tinubu ya sauya Nuhu Ribadu

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi dirar mikiya a kasuwa, an rasa rayukan mutane da dama a Neja

A wani labari, mun ruwaito cewa, Sanatan Osun ta Gabas, Francis Fadahunsi, ya roki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ci gaba da gyara tsarin tsaro.

Fadahunsi ya ce ya dace a mayar da NSA na yanzu, Mallam Nuhu Ribadu, zuwa wani bangare na gwamnati da zai fi dacewa da kwarewarsa.

Ya tunatar da cewa a baya ya yi kira da a yi gyara mai tasiri a rundunar tsaron Najeriya, yana mai jaddada cewa matsalar ita ce wadanda ke kan shugabanci ba sojoji ba ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com