2027: Ana Kulla wa EFCC Makarkashiya, Hukumar Ta Fallasa Shirin Ƴan Adawa
- EFCC ta bankado shirin 'yan siyasar adawa na bata sunan shugaban hukumar, Ola Olukoyede da sanya tsoro a tsakanin jami'anta
- Hukumar ta yi ikirarin cewa, wadannan 'yan adawa sun dage cewa sai sun ga bayan EFCC don dakile binciken rashawa da take yi
- Sai dai, hukumar yaki da rashawar ta sha alwashin cewa ba za ta tsorata ba, yayin da ta wanke kanta daga zargin nuna bangaranci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta yi ikirarin cewa ta gano makarkashiyar da ’yan siyasar adawa suke ƙulla mata.
EFCC ta ce 'yan siyasar adawar, sun dukufa wajen ganin bayan hukumar da kuma ɓata sunan shugabanta, Mista Ola Olukoyede.

Source: Twitter
EFCC ta bankado makircin wasu 'yan siyasa
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Laraba, 7 ga Janairu, 2026, a Abuja da kuma shafinta na Facebook.
A cikin sanarwar, EFCC ta ce waɗannan 'yan siyasar na ƙoƙarin amfani da dabarun tsoratarwa da yaɗa labaran ƙarya domin dakile binciken manyan laifuffukan rashawa da hukumar ke gudanarwa.
EFCC ta ce ’yan siyasar na son rudar da jama’a ne ta hanyar zargin hukumar da nuna son kai, domin su sanya tsoro a zuciyar jami’an hukumar.
Sanarwar ta ce manufar yin hakan ita ce karya gwiwar jami'an EFCC ta yadda za su ji tsoron bincikar 'yan siyasar adawa don kada a yi musu lakabi da "’yan amshin shatan gwamnati."
Sanarwar ta jaddada cewa wannan makirci da tuggu na ɓata suna zai ƙara tsananta ne yayin da kwanakin zaɓen 2027 ke ƙara gabatowa.
Hukumar EFCC ta gargadi masu son ganin bayanta
Dele Oyewale ya bayyana cewa hukumar EFCC ba za ta zuba ido tana kallon 'yan bangar siyasa suna rubuce-rubuce da maganganun karya a kanta ba.
Sannan, ya ce EFCC ba za ta amince da kowane irin yunkuri na raba hankalinta da aikin kishin ƙasa na tabbatar da gaskiya da riƙon amana ba.
Sanarwar ta jaddada cewa EFCC ba ta da alaƙa da kowace jam’iyyar siyasa, kuma tana gudanar da dukkan ayyukanta ne bisa ƙa’idojin dokar da ta kafa ta ba tare da tsoro ko alfarma ba.

Source: Facebook
'Ana binciken 'yan APC, PDP, ADC - EFCC
Hukumar ta kuma bayyana cewa a halin yanzu akwai manyan mambobin jam’iyya mai mulki (APC) da kuma na adawa (PDP & ADC) waɗanda duka suke fuskantar shari’a ko bincike a hannun hukumar.
Hakan, a cewarta, hakan shaida ce da ke nuna cewa babu wurin buya ga duk wanda yake da sa hannu a almundahana, komai matsayinsa ko jam’iyyar da yake ciki.
EFCC ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za ta ci gaba da tsayawa kan gaskiya domin kare martabar tattalin arziƙin ƙasa.
Karanta sanarwar a kasa:
Kotu ta amince EFCC ta rike kadarorin Malami
A wani labari, mun ruwaito cewa, kotu ta ba EFCC umarnin wucin gadi na ƙwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaka da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami, SAN.
Hukumar EFCC ce ta shigar da bukatar kwace kadarorin bisa zargin cewa Malami, tsohon ministan shari'a ya mallake su ta hanyar amfani da kudin haram.
Kwafin umarnin kotun da aka samu a ranar Laraba ya nuna cewa kadarorin da suka kunshi filaye da gine-ginen da abin ya shafa suna a Abuja, Kebbi, Kano da Kaduna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

