Nijar da Kasashe 2 Sun Ci Bashin Wutar Lantarkin N25bn a Najeriya Sun Gaza Biya
- Hukumar NERC ta ce kasashen Togo, Nijar da Benin ba su biya cikakken kudin wutar lantarki da suka sha daga Najeriya ba a zango na uku na 2025
- Rahoton ya nuna cewa kudin da aka biya bai kai rabin abin da ake bukata ba, lamarin da ya sake tayar da tambaya kan tsarin biyan kudi wuta a ketare
- A gefe guda kuma, hukumar NERC ta bayyana cewa abokan cinikin cikin gida Najeriya sun fi nuna hadin kai wajen biyan kudin wuta da ake bukata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya, NERC, ta bayyana cewa Najeriya na bin kasashen Togo, Nijar da Benin bashin Dala miliyan 17.8, wanda ya kai sama da N25bn.
Wannan bashi ya samo asali ne daga wutar lantarki da Najeriya ke samarwa tare da sayarwa ga wadannan kasashe bisa yarjejeniyar da suka yi.

Source: Getty Images
Bashin wuta da Najeriya ke bin kasashe
Punch ta wallafa cewa a rahotonta na zango na uku na shekarar 2025 ne NERC ta sanar da cewa tana bin kasashen Dala miliyan 18.69, amma abin da suka biya bai wuce Dala miliyan 7.125 ba.
Hukumar ta bayyana cewa baya ga bashin da ya samo asali a zango na uku na 2025, akwai kuma tsofaffin basussuka daga zangunan baya da suka kai Dala miliyan 14.7.
Daga wannan adadi, kasashen sun biya Dala miliyan 7.84, yayin da sauran Dala miliyan 6.23 suka ci gaba da zama bashi a kansu.
Jimillar bashin da ake bin kasashen ya kai Dala miliyan 17.8, wanda ya kai kimanin N25.36bn bisa la’akari da kudin musayar N1,425 ga kowace Dala.
Yadda ake biyan kudin wuta a Najeriya
Hukumar ta kwatanta halin biyan kudin kasashen ketare da na cikin gida, inda ta ce ‘yan kasuwar cikin gida sun fi nuna kwarewa da ba da hadin kai.
A zango na uku na 2025, masu sayen wuta ta yarjejeniyar cikin gida sun biya N3.19bn daga cikin N3.64bn da aka nemi su biya, wanda ya kai kashi 87.61.
Hakan ya nuna bambanci mai yawa tsakanin tsarin biyan kudin cikin gida da na ketare, duk da cewa dukkaninsu na karbar wuta daga tushen lantarki na kasa na Najeriya.

Source: Twitter
The Cable ta rahoto cewa NERC ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin abokan cinikin bangarori biyu sun biya wasu tsofaffin basusuuka da aka biyo su a zangunan baya.
An nemi masallatai su biya kudin wuta
A wani labarin, kun ji cewa kamfanin rarraba wutar lantarki na JED ya yi korafi kan yadda wasu wuraren ibada ba su son biyan kudin wuta.
JED ya ce wasu masallatai da coci-coci ba su son rika sanya musu mita domin su rika biyan kudin wutar da suka sha yadda ya dace.
Kamfanin ya yi kira ga shugabannin addini da su rika ba su hadin kai, domin a cewarsa, suna tafka asara sosai a jihar Gombe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

