Ana Tuhumar Malamin Addini kan Zargin Yunkurin Hallaka Ministan Abuja, Wike

Ana Tuhumar Malamin Addini kan Zargin Yunkurin Hallaka Ministan Abuja, Wike

  • Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cafke wani limamin addini da ake zarginsa da shirya makarkashiyar kashe minista
  • Majiyoyi suka ce an cafke malamin a birnin Port Harcourt da ke jihar Rivers bisa zargin ganin bayan ministan Abuja, Nyesom Wike
  • ‘Yan sanda sun ce bincike na ci gaba kan limamin, Tombari Gbeneol, kuma za a fitar da karin bayani bayan kammala bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce tana ci gaba da bincike kan wani limamin coci kan zargin yunkurin kisan kai.

An kama malamin ne da ke Port Harcourt, Tombari Gbeneol, wanda aka cafke bisa zargin shirya makarkashiyar kai hari ga Ministan Abuja, Nyesom Wike.

An kama Fasto da ake zargi da yunkurin hallaka Wike
Ministan Abuja, Nyesom Wike yana jawabi lokacin da ya ke gwamnan Rivers. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike.
Source: Facebook

Ana tuhumar Fasto da shirin hallaka Wike

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta kasa, Benjamin Hundeyin, ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata 7 ga watan Janairun 2026, cewarThe Nation.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Kotu ta kwace kadarori 57 na Malami a Kano, Abuja da wasu jihohi 2

Hundeyin ya tabbatar cewa za a yi karin haske bayan kammala binciken da ake yi game da zargin Faston.

A cewar Hundeyin:

“Yana hannunmu. Bincike na ci gaba. Ba zan ce komai fiye da haka ba. Bayan mun kammala bincike, za ku samu cikakken bayani.”

An bayyana cewa an cafke Gbeneol, wanda shi ne wanda ya kafa cocin Life Forte Chapel a Port Harcourt, Jihar Rivers, kusan makonni biyu da suka gabata ta hannun jami’an binciken sirri na Sufeto Janar na ‘Yan Sanda.

Majiyoyi sun ce an cafke limamin ne bayan da jami’an tsaro suka samu wata tattaunawar waya tsakaninsa da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Rivers, Dr Tammy Danagogo.

A n ce a cikin tattaunawar, ana zargin mutanen biyu, inda Gbeneol wanda kuma likita ne, suka tattauna shirin kawo ‘yan kasar Isra’ila domin kawar da Ministan Abuja.

Majiyar ta ce:

“Abin da ke cikin kiran da aka yi ya zama barazana ga tsaron kasa, shi ya sa IRT ta dauki matakin gaggawa.”
Hukumomi na tuhumar Fasto kan zargin shirya hallaka Wike
Babban sufeta-janar na yan sanda a Najeriya, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Tsohon sakataren gwamnati ya yi magana

Kara karanta wannan

Ana zargin za a kawo mutumin Isra'ila ya kashe Wike, tsohon minista ya magantu

Ko da yake wani jami’in tsaro ya ce ana kokarin cafke Danagogo, tsohon SSG din ya fitar da sanarwa ta hannun mataimakinsa na musamman, Obele Briggs, inda ya musanta zarge-zargen baki daya.

Danagogo ya ce bai buya ba, kuma zai bayyana kansa ga kowace hukuma ta tsaro idan an gayyace shi, yana mai bayyana kansa a matsayin mutum mai son zaman lafiya da bin doka.

Sanarwar ta ce:

“Dr Danagogo ya musanta wadannan zarge-zarge gaba daya. Karya ne, kirkirarre kuma an shirya su ne domin bata masa suna.”

Ya kara da cewa rahotannin da ke yawo a wasu kafafen intanet karya ne kuma marasa tushe, yana mai kira ga jama’a da su yi watsi da su baki daya, cewar Leadership.

Danagogo ya jaddada cewa:

“Ban da ni, kuma ban taba zama, mutum da ake nema ruwa a jallo ba. Ina gidana lafiya lau, kuma zan amsa duk wata gayyata daga ‘yan sanda ko wata hukuma ta shari’a.”

Kiristoci sun gargadi Wike kan siyasar Bauchi

A baya. kun ji cewa Kungiyar Christian Youth in Politics (CYP) ta Bauchi ta gargadi Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya nisanci harkokin siyasar Jihar.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun fafata da 'yan bindiga, an ceto mutanen da aka sace a Zamfara

CYP ta zargi Wike da katsalandan a siyasa, amfani da hukumomin tarayya, da matakan da ka iya barazana ga zaman lafiya a jihar.

Kungiyar ta kare Gwamna Bala Mohammed, tana cewa yana da cikakkiyar kariya ta kundin tsarin mulkin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.