Wasu 'Yan Kasuwa Sun Hade da Dangote, Za Su Kara Sauke Farashin Fetur a Najeriya
- Farashin man fetur na iya sauka zuwa kasa da N739 da zarar matatar Dangote ta fara kai kaya kyauta zuwa gidajen mai da ta kulla yarjejeniya da su
- Kungiyar 'yan kasuwa masu zaman kansu (IPMAN) ta ce da yiwuwar 'yan Najeriya su samu araha a farashin kowace lita nan gaba
- Sai dai rahoto ya nuna cewa har yanzu farashin litar fetur na haura N900 a wasu gidajen mai a Abuja da sauran jihohin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Hadin gwiwar da ke tsakanin wasu daga cikin dillalan fetur da matatar Dangote ta kara karfi kuma hakan na iya zama alheri ga 'yan Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan kasuwar mai da ke hada kai da matatar Dangote na shirin kara ruguza farashin fetur, inda ake sa ran za su sayar da kowace lita kasa da N739.

Source: Getty Images
Jaridar The Nation ta bayyana hakan a wani rahoto da ta fitar, wanda ya tabbatar da cewa matatar ta fara horar da ma'aikatan gidajen man da ta kulla yarjejeniya da su a fadin Najeriya.
Matatar Dangote ta fara horar da ma'aikata
Bayanai sun nuna cewa ma'aikatan gidajen mai sun fara daukar wannan horo ne ta yanar gizo a ranar Talata da ta gabata.
Bayan kammala horarwar, ana sa ran matatar za ta fara kai fetur kai tsaye zuwa gidajen mai ba tare da cajin kudin sufuri ba, ga dukkan gidajen mai da suka shiga wannan haɗin gwiwar.
Wasu daga cikin wadanda suka yi haɗin gwiwa da matatar sun haɗa da MRS, Ardova Petroleum (AP), Garima, Heyden da Optimal.
Premium Times ta ruwaito tun a watan Disamba cewa, ban da MRS, sauran gidajen man ba su fara sayar da fetur a farashin matatar ba ne saboda har yanzu ba su karɓi kaya daga tsarin jigila kyauta ba.
Abin da zai sa fetur ya kara sauka
Da yake magana da manema labarai ta wayar tarho, Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Mai Masu Zaman Kansu ta Ƙasa (IPMAN), Alhaji Abubakar Maigandi, ya bayyana cewa akwai yiwuwar farashin fetur ya sauka kasa da N739.
Ya ce duba da tazarar riba da ke tsakanin farashin fetur a rumbunan kasuwanci, N699 da farashin da aka yi hasashen za a sayar a gidajen mai watau N739, mai yiwuwa kawayen matatar Dangote su kara rage kudin kowace lita.
Abubakar Maigandi ya ce:
“Wasu daga cikin ’yan kasuwa da za su amfana da jigilar kaya kyauta daga Dangote na iya sayar da fetur ƙasa da ₦739 kan kowace lita.
"Idan ka duba farashin matatar na ₦699, akwai sama da ₦25 ribar da ke ba da damar rage farashi a kasuwa mai gasa.”

Source: Getty Images
Bincike ya nuna cewa a Abuja, MRS na sayar da litar fetur a ₦739 amma akwai ɗan layi, A.A. Rano na sayarwa a ₦840, Total kuma na sayarwa a ₦920, yayin da wasu ’yan kasuwa masu zaman kansu ke sayar da shi har ₦930 kan kowace lita.
Da gaske an rufe matatar Dangote?
A wani rahoton, kun ji cewa matatar mai ta Dangote da ke jihar Legas ta musanta labarin da ake yadawa cewa ta dakatar da ayyukanta na dan lokaci domin yin wasu gyare-gyare.
Matatar Dangote ta karyata rahoton, wanda wasu ke yada cewa tana shirin rufewa domin aikin gyara, inda ta bayyana labarin a matsayin ƙarya da yaudara.
Matatar ta kuma jaddada cewa farashin kowace litar man feturinta na nan a N699 ga 'yan kasuwa da masu saye kadan-kadan a fadin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


