Mutanen Gari Sun Tsinci Makami Mai Linzami a Jihar Neja, Ana Zargin na Amurka ne
- Rundunar yan sandan jihar Neja ta tabbatar da gano wani makami mai linzami a jihar Neja wanda ake zargin na kasar Amurka ne
- Mazauna yankin Zugurma sun shiga tashin hankali bayan ganin makamin a daji inda nan take jami'an kwance bam suka isa wajen
- Yan Najeriya da dama sun fara tofa albarkacin bakinsu kan hatsarin da wadannan makaman da basu fashe ba ke tattare da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - An shiga yanayi na zaman dar-dar da fargaba a yankin Zugurma da ke ƙaramar hukumar Mashegu a jihar Neja, biyo bayan gano wani makami mai linzami.
An ruwaito cewa, mazauna yankin Zugurma ne suka gano wannan makami mai linzami da bai riga ya tashi ba a ranar Litinin, 5 ga watan Janairu, 2026.

Kara karanta wannan
Makiyaya dauke da makamai sun mamaye garuruwa 2 a Benue, mutane sun shiga fargaba

Source: Twitter
An tsinci makami mai linzami a Neja
Mutanen sun yi karo da wannan ƙaton ƙarfe a cikin daji, inda nan take suka gane cewa ba ƙaramin abu ba ne, hakan ya sa suka garzaya domin sanar da jami’an tsaro mafi kusa, in ji rahoton Daily Trust.
Ana fargabar cewa makamin da ake zargin nau’in Tomahawk ne, yana ɗaya daga cikin makaman Amurka da aka harba a kwanakin baya yayin wani farmaki kan sansanonin ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.
Kodayake Amurka ta ce ta yi amfani da makamai masu amfani da fasaha, tsinto wannan makami da bai fashe ba ya tayar da hankulan mazauna yankin kan hatsarin da hakan ke tattare da shi ga rayuwar talakawa.
Martanin 'yan sanda kan ganin makami mai linzami
Kakakin rundunar ’yan sandan Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar wa manema labarai cewa kwamishinan ’yan sandan jihar, Adamu Elleman, ya bayar da umarnin gaggawa na tura ƙwararru zuwa wurin.
Jami'an sashin kwance bama-bamai (EOD-CBRN) ƙarƙashin jagorancin CSP Mohammed Mamun, sun isa yankin na Zugurma a ranar Talata, inda suka katange wurin don gudun kada mutane su kusanci makamin.
Jami'an sun yi nasarar kwance makamin tare da kwashe shi zuwa babban ofishin ’yan sanda da ke birnin Minna domin ci gaba da bincike, in ji rahoton Vanguard.

Source: Original
'Yan Najeriya sun nuna damuwarsu
Wannan lamari ya janyo ce-ce-ku-ce mai zafi a tsakanin ’yan Najeriya a kafafen sada zumunta. Mutane da dama sun nuna fargabar cewa ko Amurka na amfani da ƙasar Najeriya ne a matsayin wurin gwajin sababbin makamanta.
Wasu kuma sun nuna damuwa kan yadda makaman da ba su fashe ba (UXO) za su iya zama babban haɗari ga manoma da makiyaya a yankunan karkara.
Rundunar ’yan sanda ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu, tana mai tabbatar da cewa tana yin duk abin da ya dace don tabbatar da tsaron yankunan da abin ya shafa.
Mutane sun fara tserewa daga gidajensu
A wani labari, mun ruwaito cewa, mazauna yankunan karkara a ƙananan hukumomin Agwara da Borgu a jihar Niger na cikin tashin hankali da zaman dari-dari.
Mazauna waɗannan yankuna sun fara tserewa daga gidajensu sakamakon barazanar da ’yan bindiga suka yi na cewa za su dawo domin ci gaba da yi masu kisan gilla.
Wannan fargaba ta ƙaru ne biyo bayan harin ranar Asabar, 3 ga watan Janairu, 2026, inda aka kashe mutane 42, sannan aka yi garkuwa da mata da yara da dama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

