Kotu Ta ba Abubakar Malami, Matarsa da Dansa Beli, za Su Biya N1.5bn
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da bayar da beli ga tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami da matarsa da dansa, amma da tsauraran sharuda
- Kotun ta tanadi sharudan mallakar kadarori a manyan unguwanni tare da mika takardun biza, yayin da ake ci gaba da tsare su har sai sun cika sharudan
- Shari’ar na da alaka da zargin karkatar kadarori na biliyoyin Naira, lamarin da ya janyo hankalin jama’a da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da bayar da beli ga tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, tare da matarsa da dansa, inda kotun ta gindaya sharuda masu tsauri kafin su samu ‘yanci.
Alkalin kotun, Mai shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin bayar da belin ya ce kowanne daga cikin wadanda ake tuhuma zai bayar da Naira miliyan 500 a matsayin beli.

Source: Facebook
Hukumar EFCC ta wallafa a Facebook cewa kotun ta ce za su ci gaba da kasancewa a tsare har sai sun kammala cika dukkan sharudan belin da aka shimfida musu.
Sharudan belin Abubakar Malami da iyalansa
Mai shari’a Nwite ya bayyana cewa dole masu tsayawa a belin su kasance masu kadarori a unguwannin Asokoro, Maitama da Gwarinpa da ke Abuja.
Kotun ta kara da cewa dole ne a mika takardun kadarorin domin tantancewa, inda mataimakin babban magatakardar kotu zai tabbatar da sahihancinsu.
Kotu ta kakaba takunkumin tafiye-tafiye ga Malami
Rahoto Channesl Television ya nuna cewa kotun ta kuma umurci Abubakar Malami da ya mika dukkan takardun balaguronsa.
An bayyana cewa ba zai fita daga Najeriya ba sai da izinin kotu, domin tabbatar da cewa zai rika halartar zaman shari’a yadda doka ta tanada.
Wannan umarni ya shafi sauran wadanda ake tuhuma tare da shi, domin kotu ta hana duk wani yunkuri da zai iya kawo cikas ga shari’ar.

Kara karanta wannan
Yunkurin juyin mulki: Yadda sojoji suka kama Shehin malami, Khalifa Zariya a Abuja
Zarge-zargen da ake yi wa Malami
Abubakar Malami, wanda ya rike mukamin Ministan Shari’a daga 11, Nuwamba, 2015 zuwa 29, Mayu, 2023 a karkashin gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, na fuskantar tuhume-tuhume har guda 16.
An gurfanar da shi ne tare da dansa Abdulaziz da matarsa Asabe, wadda aka bayyana a matsayin ma’aikaciya a kamfanin Rahamaniyya.

Source: Facebook
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce ana zargin wadanda ake tuhuma da karkatar da kudin jama’a da yawansu ya kai kusan Naira biliyan 9.
Wasu rahotanni sun kara da cewa kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 17, Fabrairun 2026 domin cigaba da sauraron korafe-korafe.
An hana belin kwamishinan Bauchi
A wani labarin, mun kawo muku cewa wata kotun tarayya ta hana kwamishinan kudin jihar Bauchi beli bayan zaman da ta yi a Abuja.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da kwamishinan bisa zarge-zarge da dama da ke da alaka da cin hanci da rashawa da karkatar da kudi.
Daga cikin zarge-zargen akwai zargin daukar nauyin ta'addanci, amma gwamna Bala Mohammed ya karyata batun, inda ya ce yana goyon bayan zaman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
