Tinubu Ya Naɗa Mace Ta Farko a Matsayin Shugabar Makarantar Horas da Lauyoyi
- Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya naɗa Olugbemisola Odusote a matsayin sabuwar Shugaba ta makarantar horarda lauyoyi ta Najeriya
- Naɗin ya fara aiki ne daga 10 ga Janairu, 2026, kuma zai ɗauki tsawon shekaru huɗu kamar yadda ya ke a tsarin kasa
- Odusote za ta zama mace ta farko da za ta jagoranci makarantar tun kafuwarta a 1962 kuma za ta gaji Isa Chiroma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Olugbemisola Odusote a matsayin sabuwar Shugaba ta makarantar horar da lauyoyi ta Najeriya.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Source: Facebook
Channels TV ta wallafa cewa sanarwar ta ce naɗin zai fara aiki daga ranar 10 ga Janairu, 2026, kuma an tsara wa’adin ne na tsawon shekaru huɗu.
Bola Tinubu ya yi sabon naɗin mukami
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa a matsayinta na Shugaba, Odusote za ta kasance mai jagorantar harkokin ilimi gaba ɗaya.
Haka kuma za ta kuma da tafiyar da harkokin gudanarwa, da kuma tsara alkiblar ci gaban makarantar a dukkan rassanta da ke faɗin ƙasar nan.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa Odusote za ta zama babbar hanyar haɗin gwiwa tsakanin makarantar lauyoyi ta Najeriya.
Za kuma ta yi aiki da hukumar koyar da Ilimin lauya, Majalisar masu nada lauyoyi da kuma kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA).
Ana ganin wannan matsayi zai ba ta damar tabbatar da daidaito da ingancin horon lauyoyi a ƙasar da kuma inganta aikin lauya baki daya.
Wace ce Odusote da Tinubu ya naɗa?
A cewar sanarwar, Olugbemisola Odusote mai shekaru 57 za ta gaji Isa Chiroma, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar 9 ga Janairu, 2026, bayan ya shafe shekaru takwas yana jagorantar makarantar.
Da wannan naɗi, Odusote za ta zama mace ta farko da ta taɓa rike muƙamin jagorancin makarantar hoton lauyoyi ta Najeriya tun bayan kafuwarta a shekarar 1962.
A halin yanzu, Odusote ita ce mataimakiyar Darakta-Janar kuma shugabar reshen Legas na makarantar. Ta fara karatunta na digiri a fannin shari’a a Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU).

Source: Twitter
A wannan jami'a ne kuma ta kammala karatu kuma ta zama cikakkiyar lauya a shekarar 1988. Ta samu digirin digirgir daga jami’ar, inda ta ƙware a harkokin kamfanoni da kasuwanci.
Odusote ta samu digirin digirgir na uku (PhD) a fannin shari’a daga Jami’ar Surrey da ke Birtaniya, inda bincikenta ya mayar da hankali kan dokar jama’a da gudanar da adalci.
Ta shiga Makarantar Lauyoyi ta Najeriya a matsayin malama a 2001, kuma ta haura matakai daban-daban na aiki, ciki har da shugabar sashen ilimi, daraktar harkokin ilimi, da shugabar harabar makaranta.
Naɗin nata na zuwa ne a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa shugabanci da bunƙasa tsarin koyar da ilimin shari’a a Najeriya.
Tinubu ya ba Mahmud Yakubu muƙami
A baya, kun ji cewa tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu ya samu sabon mukami a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wannan naɗi ya nuna ci gaba da amincewar gwamnatin tarayya da ƙwarewarsa a harkokin gudanarwa da hidimar ƙasa jim kaɗan bayan ya ajiye mukaminsa a INEC.
Naɗin Farfesa Yakubu na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ke ci gaba da gyara da sake fasalin manyan muƙamai a cikin gwamnatin sa, musamman a ɓangaren hulɗar ƙasa da ƙasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


