Ana Zargin za a Kawo Mutumin Isra'ila Ya Kashe Wike, Tsohon Minista Ya Magantu

Ana Zargin za a Kawo Mutumin Isra'ila Ya Kashe Wike, Tsohon Minista Ya Magantu

  • Tsohon Ministan Wasanni, Dr. Tammy Danagogo, ya fito ya karyata zargin cewa yana da hannu a shirin kashe ministan Abuja, Nyesom Wike
  • An ce 'yan sanda sun kama wani likita kuma fasto a Rivers bisa zargin shirya kisan, amma bincike na cigaba da gudana kan lamarin
  • Tammy Danagogo ya ce zarge-zargen kirkirarru ne, yana mai jaddada cewa yana shirye ya ba da hadin kai ga masu bincike a Rivers

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers – Tsohon Ministan Wasanni kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Rivers, Dr. Tammy Danagogo, ya karyata zargin cewa yana da hannu a wani shiri na kashe Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike.

Zargin ya biyo bayan kama wani likita kuma wanda ya kafa cocin Life Forte Chapel a Port Harcourt, Tombari Gbeneol da jami'an tsaro suka yi.

Kara karanta wannan

Kano: Wasu yara sun fadi dalilin murna da rasuwar mahaifinsu bayan shekaru 20

Tammy Danagogo da Nyesom Wike
Tsohon SSG na Rivers, Tammy Danagogo da Ministan Abuja, Nyesom Wike. Hoto: Lere Olayinka|Obele Briggs
Source: Facebook

Rahoton Leadership ya ce an kama Gbeneol ne bisa zargin shirin kashe Wike, lamarin da ya kara tayar da hankula a fagen siyasa da tsaro a Rivers da Abuja.

Yadda maganar kashe Wike ta bayyana

An bayyana cewa kama faston ya biyo bayan samun wata magana ta waya da ake ikirarin ta gudana tsakaninsa da Danagogo, wanda shi ne tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Rivers.

A cikin maganar da aka ce sun yi, ana zargin cewa an tattauna shirin kawo dan kasar Isra’ila domin aiwatar da kashe Ministan FCT.

Rahoton ya kara da cewa tattaunawar ta kare da wani shiri na neman tallafin kudi daga Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, domin aiwatar da shirin.

Maganar Danagogo kan shirin kashe Wike

Sai dai a wata sanarwa da aka fitar a Port Harcourt da yammacin Litinin, Danagogo ya yi watsi da zargin, yana mai bayyana shi a matsayin kirkirarren labari maras tushe.

Kara karanta wannan

Rigima ta kara zafi, sakataren APC na kasa ya nemi Ministan Tinubu ya yi murabus

Punch ta rahoto cewa sanarwar da hadiminisa na musamman, Barrista Obele Briggs, ya sanya wa hannu, ta ce tsohon ministan bai taba shiga wata tattaunawa ko shiri da ya shafi tashin hankali ko kisan kai ba.

Sanarwar ta ce an jawo hankalin Danagogo kan sakon da ke yawo a kafafen intanet da ke zargin sa da hada baki da Fasto Tombari Gbeneol wajen shirya kisan.

Nyesom Wike da Sanata Goodswill Akpabio
Ministan Abuja, Nyesom Wike da Sanata Godswill Akpabio. Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

Obele Briggs ya ce wadannan zarge-zarge karya ne tsagwaron su, an kirkire su ne domin bata masa suna da ya gina tsawon shekaru.

A cewar sanarwar, Danagogo mutum ne mai son zaman lafiya, mai bin doka, wanda ya yi wa Jihar Rivers da Najeriya hidima cikin gaskiya da mutunci.

An zargi Wike da raina sarakuna

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar 'yan asalin birnin tarayya Abuja ta zargi Ministan FCT, Nyesom Wike da raina dattawa.

Kungiyar ta ce ministan ba ya girmama sarakuna da masu ruwa da tsaki a Abuja tun bayan ba nada shi da shugaba Bola Tinubu ya yi.

Sanarwar da mutannen Abuja suka fitar ta nuna cewa Wike ya zauna da sarakuna a Rivers amma bai taba yin zama da na Abuja ba ko sau daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng