Yadda Aka Kashe Wani Uban Daba a Kano da Rikici Ya Barke tsakanin Unguwanni 2

Yadda Aka Kashe Wani Uban Daba a Kano da Rikici Ya Barke tsakanin Unguwanni 2

  • Rikicin 'yan daba a Kano ya yi sanadiyyar mutuwar wani uban daba bayan an labta masa sara a wuya yayin wani harin daukar fansa
  • Jami'an yan sanda sun yi nasarar kama mutane tara tare da tarwatsa wasu 'yan daba da suka yi kokarin sake tada yamutsi a Mariri
  • Rundunar tsaro ta tabbatar da cewa al'amura sun lafa a yankin Kawo yayin da ake ci gaba da neman sauran yan daban da suka tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - An tabbatar da mutuwar mutum guda yayin da aka kama wasu mutane tara biyo bayan wani kazamin rikici tsakanin wasu ƙungiyoyin ’yan daba biyu a Kano.

Kungiyoyin dabar biyu da ke a yankunan Kawo da Mariri da ke cikin birnin Kano sun barke da fada a tsakaninsu ne a daren ranar 4 ga Janairu, 2025.

Kara karanta wannan

Kano: Wasu yara sun fadi dalilin murna da rasuwar mahaifinsu bayan shekaru 20

Fadan daba ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum 1 a Kano
Rundunar 'yan sandan Kano ta baje kolin wasu matasa da aka kama da zargin ayyukan daba. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Fadan daba ya barke a wasu yankunan Kano

Zagazola Makama, mai sharhi kan lamuran tsaro a Arewacin Najeriya da Tafkin Chadi ne ya rahoto labarin a shafinsa na X.

Rahoton ya nuna cewa fadan ya kaure ne tsakanin ƙungiyar uban daba Kabalo Snu da kuma ƙungiyar uban daba Faizu Mohammed, wanda aka fi sani da "Chabross" na Yar Kasuwa, a yankin Kawo.

Rikicin ya samo asali ne daga wani farmakin ɗaukar fansa bayan da Faizu Mohammed ya fara raunata Kabalo a wani saɓani da suka yi da rana da misalin ƙarfe 1:40.

Wannan harin na rana ya fusata magoya bayan Kabalo, inda suka shirya gagarumin harin ramuwar gayya da misalin ƙarfe 9:00 na dare.

A yayin fafatawar, an soki Faizu Mohammed a wuya da wani abu mai kaifi, inda ya sami raunuka masu tsanani, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida.

Mutuwar uban daba da abin da ya biyo baya

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun fafata da 'yan bindiga, an ceto mutanen da aka sace a Zamfara

An garzaya da Chabross asibitin ƙwararru na Sir Muhammadu Sanusi, inda ya cika yayin da ake ƙoƙarin ceto rayuwarsa. Bayan rasuwarsa, an miƙa gawar sa ga iyalansa domin binnewa.

Sai dai, mutuwar Chabross ta harzuka wasu 'yan dabar da ke cikin gungunsa, wadanda suka shirya wani mummunan harin daukar fansa kan dabar Kabalo.

A safiyar ranar 5 ga watan Janairu, 2025 ne aka samu rahoton cewa fusatattun yaran marigayi Chabros sun taru a Kawo domin kai harin ramuwa gidan su Kabalo dake yankin Jar Kuka, Mariri.

An tabbatar da cewa an cafke akalla mutane 9 bayan an kashe wani uban daba a Kano
Taswirar jihar Kano, inda aka kashe uban daba Chabross a rikin kungiyoyin daba 2. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun cafke 'yan daba 9

Rahoton ya nuna cewa jami'an 'yan sanda sun isa yankin Jar Kuka, Mariri cikin gaggawa inda suka tarar 'yan dabar Chabross har sun farfasa shagon Kabalo.

’Yan sandan sun yi nasarar tarwatsa su tare da kama mutane tara daga cikinsu, yayin da wasu da dama suka ranta a na-kare.

Zuwa yanzu, jami'an tsaro sun bayyana cewa al'amura sun daidaita a yankunan da abin ya shafa, kuma an kwace wasu makaman da ’yan daban suka yi amfani da su.

Fadan daba: Mata sun fito zanga-zanga a Kano

Kara karanta wannan

'Mutane sun fara guduwa,' Halin da ake ciki a Neja bayan kashe fiye da mutum 40

A wani labari, mun ruwaito cewa, mata sun yi zanga-zanga a Kofar Mata domin nuna damuwarsu kan rikice-rikicen ‘yan daba da ke ci gaba da kashe mutane.

Sun bukaci gwamnati da hukumomin tsaro da su gaggauta daukar mataki domin dakile rikice-rikicen da suka yi kamari tsakanin ‘yan daba.

Masu zanga zangar sun ce sun ɗauki matakin fito wa kan tituna bayan da ƴan daba suka jera kusan kwanaki biyar suna ɗauki ba daɗi, suna firgita mutane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com