Ministan Tinubu Ya Kare Kansa bayan Zargin Batan N128bn a Hannunsa

Ministan Tinubu Ya Kare Kansa bayan Zargin Batan N128bn a Hannunsa

  • Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya yi martani bayan zargin ɓatan ₦128bn da kungiyar SERAP ta bankado yanzu
  • Adelabu ya bayyana cewa rahoton binciken da SERAP ke dogaro da shi ya faru a shekarar 2022, kafin zuwan gwamnatin Bola Tinubu
  • Ma’aikatar Makamashi ta tarayya ta ce tana maraba da bincike, tare da jaddada kudirinta na gaskiya da riƙon amana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan makamashi, Cif Adebayo Adelabu, ya magantu kan zargin batan N128bn da kungiyar SERAP ta bankado.

Adelabu ya ce zargin ɓata ko karkatar da ₦128bn na kuɗaɗen jama’a da ƙungiyar ke magana a kai ya faru ne kafin a nada shi a matsayin minista.

Minista ya kare kansa kan zargin badalakar N128bn
Ministan makamashi a Najeriya, Adebayo Adelabu. Hoto: Bayo Adelabu.
Source: Facebook

Minista ya karyata zargin wawure N128bn

Adelabu ya bayyana hakan ne bayan SERAP ta bukaci Bola Ahmed Tinubu da ya umarci binciken batan kudaden a hannunsa, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Tsohon dan majalisa da aka sace a masallaci ya samu 'yanci bayan biyan N50m

Sanarwar SERAP ta bukaci a umarci Ministan Shari’a tare da hukumomin yaƙi da cin hanci, su binciki zargin ɓatan kuɗaɗen daga Ma’aikatar Wutar Lantarki da kuma Kamfanin NBET.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Bolaji Tunji, ya fitar, an ce rahoton binciken da SERAP ke dogaro da shi ya shafi shekarar 2022 ne kaɗai.

Ya ce lokacin bai zama minista a wannan gwamnati ba kuma an tabbatar da nadin Adelabu ne a watan Agustan shekarar 2023, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce, duk da cewa ministan ba ya adawa da a gudanar da bincike, amma ya zama dole a fayyace cewa batutuwan da rahoton ya ƙunsa ba su da alaƙa da ayyukan ma’aikatar a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

Ana zargin batan N128bn a hannun ministan Tinubu
Ministan makamashi a Najeriya, Adebayo Adelabu. Hoto: Bayo Adelabu.
Source: Twitter

Martanin ma'aikatar makamashi kan zargin

Ofishin Ministan makamashi ya jaddada cewa zai ba da cikakken haɗin kai ga duk wani sahihin bincike, musamman kan matsalolin da aka gada a ɓangaren wutar lantarki.

Sanarwar ta kara da cewa Adelabu sananne ne wajen bin doka, gaskiya, rikon amana da ɗa’a, kamar yadda ya nuna a mukaman da ya rike a baya.

Kara karanta wannan

Tsohuwar ministar Buhari ta faɗi waɗanda suka yi kutun kutun ta rasa kujerarta

Sanarwar ta ce:

“Mai Girma Ministan Makamashi, Cif Adebayo Adelabu, ba ya adawa da kiran a gudanar da bincike, yana da muhimmanci a fayyace cewa an naɗa shi ne a watan Agustan 2023, yayin da rahoton binciken kuɗi da ake magana a kai ya shafi shekarar 2022.”

Ma’aikatar ta ce, yayin da ake magance matsalolin da aka gada, ministan da tawagarsa za su ci gaba da mayar da hankali kan cika alkawarin samar da ingantacciyar wutar lantarki ga ‘yan Najeriya.

Minista ya zargi malami da damfara

A baya, mun ba ku labarin cewa Ministan makamashi, Bayo Adelabu, ya zargi malamin addinin Kirista da neman karbar makudan kudi a gare shi.

Adelabu ya zargi Elijah Ayodele da neman N150m domin ya taimaka masa zama gwamnan Oyo.

Adelabu ya kai kara ga DSS da ‘yan sanda, yana zargin limamin da yunkurin tada fitina da annabtar karya wanda yake amfani da hakan domin damfarar mutane.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.