An Hango Jirgin Yakin Amurka Ya Sauka a Najeriya da Dare
- Rahotanni sun nuna cewa jirgin yakin Amurka samfurin US Air Force C-130 ya sauka a Abuja da dare, kafin daga bisani ya sake tashi
- Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun karin zirga-zirgar jiragen yakin Amurka a yankin Yammacin Afirka, musamman Ghana da Senegal
- Masana tsaro na ganin tsarin zirga-zirgar na iya nuni da kara kaimi ga ayyukan yaki da ‘yan ta’adda a Najeriya da nahiyar Afirka baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa wani jirgin yakin Amurka samfurin US Air Force C-130 ya sauka a filin jirgin sama na Abuja a daren Litinin 5 ga Disamba, 2025 lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a.
Shaidu sun ce jirgin ya sauka da misalin karfe 11:00 na dare kafin daga bisani ya sake tashi, amma har yanzu babu wata sanarwa a hukumance.

Source: Twitter
DW Hausa ta wallafa a Facebook cewa wannan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan rahotannin hare-haren da Amurka ta kai wa ‘yan ta’adda a wasu yankunan Najeriya da kama shugaban Venezuela.
Bayyanar jirgin a Amurka a Najeriya
Masu bibiyar zirga-zirgar jiragen sama sun yi hasashen cewa jirgin ya fito ne daga Dakar a kasar Senegal, inda ya sauka a Abuja na dan lokaci.
An ce irin wadannan jiragen yakin Amurka galibi ana ganinsu ne a kasashen Ivory Coast ko Ghana, ba kasafai suke sauka a Najeriya kai tsaye ba.
Rahoton ya kara nuna cewa jirgin da aka gani samfurin C-130J ne, mai lambar rajista 08-3176, wanda ake amfani da shi wajen jigilar kayayyakin soja da sojoji a manyan ayyukan tsaro.
Abin da masana tsaro ke cewa
Wani masanin tsaro, Philip Brant, ya wallafa a X cewa rundunar sojin saman Amurka ta kara yawan zirga-zirgar jiragen kaya zuwa Ghana a cikin watan da ya gabata.
A cewarsa, yawancin jiragen suna tashi ne daga Djibouti, cibiyar AFRICOM ta Amurka a Afirka, dauke da kaya masu nauyi, su isa Ghana, sannan su koma Djibouti babu kaya.
Brant ya ce wannan tsari na nuni da cewa ana iya jigilar manyan kayayyakin soja, ciki har da jiragen leken asiri marasa matuka, daga sansanin Camp Lemonnier na Amurka a Djibouti zuwa Ghana.

Source: Getty Images
Mai sharhi kan tsaron ya bayyana cewa daga nan ne ake hasashen Amurka na gudanar da ayyukan yaki da ta’addanci da suka shafi Najeriya.
Najeriya ta yi shiru kan kama Maduro
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya ta yi kakkausar suka kan shirun da gwamnatin Bola Tinubu ta yi game da lamarin.
Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya ce abin kunya ne a ce Najeriya ta gaza fitar da matsayarta kan matakin da Donald Trump ya dauka a Venezuela.
Gwamnatin Trump ta kai hari kasar Venezuela tare da kama shugaban kasa Nicolas Maduro kan zarginsa da safarar miyagun kwayoyi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

