Bayan Barin Kujerar Minista, Badaru Ya Magantu kan Jita Jitar Watsar da APC
- Tsohon Ministan Tsaro a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya yi karin haske game da rade-radin cewa zai bar APC
- Badaru ya karyata jita-jitar cewa yana shirin barin APC zuwa jam’iyyar ADC bayan ya yi murabus daga kujerar minista
- Ya bukaci ‘yan Najeriya da mambobin APC su yi watsi da rahotannin, yana cewa ba shi da niyyar ficewa daga jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Ministan Tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi magana game da jita-jitar barin APC mai mulkin Najeriya.
Badaru ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa yana tattaunawa domin sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa ADC.

Source: Twitter
Badaru ya magantu kan jita-jitar barin APC
Hakan na cikin wata sanarwa da Badaru ya sanya wa hannu da Tribune ta samu a ranar Talata 6 ga watan Janairun 2026 da muke ciki.
Tsohon ministan ya bayyana cewa rahoton ƙarya ne tsagwaro, mara tushe kuma aikin masu neman tayar da hankalin siyasa ne kawai.
Sanarwar ta bayyana cewa Badaru har yanzu yana tare da APC, jam’iyyar da ya taimaka wajen kafawa tun farko, inda ya jaddada cewa biyayyarsa ga jam’iyyar cikakkiya ce kuma babu ja da baya.
Ya ce babu wata gaskiya ko kadan a cikin rade-radin da ke cewa yana shirin komawa wata jam’iyya, yana mai kiran rahotannin da ƙirƙirarru da ke neman kawo ruɗani a siyasa.

Source: Facebook
Shawarar da Badaru ya ba al'umma, 'yan jam’iyya
Tsohon ministan ya bukaci al’ummar Najeriya da mambobin APC da su yi watsi da irin wadannan rahotanni, yana mai cewa ba su da tushe kuma ba su wakiltar matsayinsa game da jam'iyyar.
Ya kara da cewa har yanzu shi cikakken ɗan APC ne, kuma ba shi da wata niyya ko shiri na barin jam’iyyar a kowane lokaci.
Rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun yawaitar jita-jitar sauya sheka a fagen siyasar Najeriya, musamman yayin da ake tunkarar shirye-shiryen siyasa gabanin manyan zaɓukan da ke tafe.
Badaru ya jaddada cewa irin wadannan jita-jita na iya rikita hankalin jama’a, amma ya ce matsayinsa a APC a bayyane yake kuma ba shi da wata shakka.
Ya jaddada goyon bayansa ga Bola Tinubu da gwamnatinsa duba da irin ayyukan alheri da shugaban ke yi wa al'ummar kasa baki daya, cewar TVC News.
Badaru ya magantu game da dalilin murabus dinsa
A baya, an ji cewa tsohon Ministan Tsaro a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya yi karin haske game da yada jita-jita bayan ya yi murabus.
Badaru ya karyata rahoton bogi da ya ce ya yi murabus ne saboda bai son hare-haren Amurka da gwamnatin Bola Tinubu kan yan bindiga.
Ya bayyana labarin a matsayin sharri da ƙoƙarin bata masa suna tare da haddasa sabani tsakaninsa da Shugaba Tinubu da gwamnatin tarayya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

