ADC na Zuga Tinubu Ya Cire Tsoro Ya Yi Martani kan Harin Trump a Venezuela
- Jam’iyyar ADC ta bayyana rikicin Venezuela a matsayin darasi ga Najeriya, tana sukar rashin bayyana matsayar gwamnatin tarayya kan kama Nicolas Maduro
- ADC ta ce shiru da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi ya nuna faduwar martabar Najeriya a idon duniya, tare da janyo tambayoyi kan sahihancin jagoranci a kasar
- Jam’iyyar ta jaddada cewa rikicin ya fallasa illar zabuka marasa inganci da gwamnatoci da ba su da cikakken goyon bayan jama’a ke yi a tsarin dimokuradiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Jam’iyyar ADC ta soki shiru da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi dangane da kama shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, tare da matarsa da Amurka ta yi.
Jam’iyyar ta bayyana cewa abin da ya faru a Venezuela ya kamata ya zama darasi ga Najeriya da sauran kasashen duniya, musamman game da sahihancin zabe.

Kara karanta wannan
Yunkurin juyin mulki: Yadda sojoji suka kama Shehin malami, Khalifa Zariya a Abuja

Source: Facebook
Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi ya wallafa a X cewa rashin mayar da martani daga gwamnatin tarayya, sabanin yadda wasu kasashe da shugabannin duniya suka yi, abin kunya ne.
Dalilin ADC na sukar gwamnatin Bola Tinubu
Bolaji Abdullahi ya bayyana a wata sanarwa cewa kama Maduro da Amurka ta yi ya nuna yadda duniya ke kara kin amincewa da gwamnatocin da ake zargi da rashin halacci da kuma zabuka marasa inganci.
A cewarsa, shiru da gwamnatin Najeriya ta yi ya nuna fargabar shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ADC ke zargin yana tsoron kada wata rana ya tsinci kansa a irin halin da Maduro ya shiga.
Abin da ADC ta ce kan kama Maduro
ADC ta bayyana cewa aikin da Amurka ta yi na kama shugaba Venezuela da matarsa a matsayin gargadi mai karfi ga dukkan gwamnatoci marasa adalci.
Jam’iyyar ta ce duk da muhimmancin kare ikon kasashe da rashin tsoma baki a harkokin cikin gida, bai kamata a yi amfani da wannan hujja wajen kare zalunci ko magudin zabe ba.
Ta jaddada cewa zabukan shugaban kasa na Venezuela da aka gudanar a 2024 sun fuskanci suka daga kasashe da kungiyoyi da dama, inda aka bayyana su a matsayin marasa inganci.

Source: Getty Images
ADC ta ce hana ‘yan adawa takara, murkushe zanga-zanga, da amfani da hukumomi wajen danniya sun haifar da ficewar jama’a daga kasar da yawa.
A cewar ADC, shiru da gwamnatin Najeriya ta yi fiye da sa'ao'i 48 bayan faruwar lamarin ya kara tabbatar da cewa gwamnatin APC karkashin Bola Tinubu ta rasa matsayi da kima a idon duniya.
Agajin da Isra'ila za ta kawo Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa kasar Isra'ila ta yi karin bayani game da maganar Benjamin Netanyahu na cewa zai kawo agaji Najeriya.
Jakadan Isra'ila a Najeriya ya ce za su tattauna da gwamnatin Bola Tinubu domin kawo tallafin da ya dace wajen yaki da 'yan ta'adda.
Ya kara da cewa za su kawo dauki ne domin kare dukkan 'yan Najeriya da suka hada da mabiya addinin Kirista da Musulmai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
