Yunkurin Juyin Mulki: Yadda Sojoji Suka Kama Shehin Malami, Khalifa Zariya a Abuja
- Iyalan Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zariya sun bayyana halin damuwa da fargaba da suka tsinci kansu a ciki tun bayan tsare malamin a Abuja
- Matar malamin ta ce tun bayan tafiyarsa Abuja kwana 25 da suka wuce, ba ta sake jin duriyarsa ba, lamarin da ya jefa su cikin tashin hankali
- Iyalansa sun ce ana tuhumar malamin ne da karbar kuɗi Naira miliyan 2, inda har yanzu ba su san inda ake tsare da shi ba ko halin da yake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna – Iyalan Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zariya sun bayyana halin ƙunci da damuwa da suka shiga tun bayan da aka tsare shi a Abuja bisa zargin karɓar kuɗin da ake alaƙantawa da addu’ar juyin mulki a Najeriya.
Uwargidar malamin ta bayyana cewa tun bayan tafiyarsa Abuja, rayuwarsu ta rikice, inda take fama da fargaba, tashin hankali da kuma damuwar da ta shafi lafiyarta.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da malamin ne a wani bidiyo da RFI Hausa ta wallafa a Facebook bayan hira da matar shi da dan shi.
Maganar matar Sheikh Khalifa Zariya
Matar Sheikh Sani Khalifa ta ce malamin ya bar gida ne da asuba, yana gaya mata cewa zai je Abuja domin wata magana ta kuɗi kuma zai dawo a ranar.
Ta ce:
“Tun daga ranar da ya tafi har yau kwana 25 kenan, bai dawo ba.”
Ta bayyana cewa wannan yanayi ya jefa ta cikin matsanancin tashin hankali, inda take ƙoƙarin daurewa kada hankalin ‘ya’yanta ya tashi.
Matar Sheikh Khalifa Zariya ta ce tana fuskantar matsalar lafiya sakamakon damuwa, har ta kai ga jin jiri da kuma buƙatar zuwa asibiti.
Yadda aka kama Sheikh Khalifa Zariya
Ɗan malamin ya bayyana cewa matsalar ta fara ne lokacin da mahaifinsa ya nemi a cire masa kuɗi daga asusunsa, inda suka je banki aka sanar da su cewa EFCC ta rufe shi.
Ya ce bayan sun tafi Abuja domin neman a buɗe asusun, an yi musu tambayoyi tare kawo bayanan tarihin kuɗin da aka tura asusun. EFCC ta ce tana tuhumar mahaifinsa ne kan kuɗi Naira miliyan 2 da aka tura masa.
A cewar dan malamin, Sheikh Khalifa ya karɓi kuɗin ne domin addu’a, sannan daga baya aka raba su a matsayin sadaka ga almajirai.
Ya ce EFCC ta kira sojoji tare da sanar da su cewa za a cire kuɗin daga asusun a mayar da shi Babban Bankin Najeriya (CBN), kuma mahaifinsa ya amince da hakan.

Source: Twitter
Ɗan malamin ya ce bayan amincewar da aka yi, sai sojoji suka ce suna da wasu tambayoyi ga malamin, daga nan kuma suka tafi da shi. Ya ce tun daga wannan lokaci ba su sake ganinsa ba.
Ya bayyana cewa an ba shi damar yin waya da mahaifinsa sau ɗaya kacal, amma har yanzu iyalan ba su san inda yake ba ko irin halin da yake ciki.
Martani kan zargin juyin mulki
Dangane da maganar juyin mulki, ɗan malamin ya ce sojoji ba su bayyana musu cewa saboda juyin mulki aka kama mahaifinsa ba.
Ya kara da cewa su ma ba su san ko soja ne ya tura masa kuɗin ba, domin ta wayar tarho kawai aka yi mu’amala da wanda ya turo masa kudin.
An nemi a saki Sheikh Khalifa Zariya
A wani labarin, kun ji cewa ana cigaba da maganganu kan kama malamin Musulunci, Sheikh Sani Khalifa Zariya da aka yi a Najeriya.
Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta bukaci hukumomi su gaggauta masa adalci tare da sake shi ya koma cikin iyalan shi.
Wasu rahotanni na cewa an kama malamin ne bisa zargin karbar kudi Naira miliyan 2 domin yin addu'ar samun nasara kan wani aiki da suka so yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


