Isra'ila Ta Fadi Abin da za Ta Yi a Najeriya idan Ta Shigo Kare Kiristoci
- Jakadan Isra’ila a Najeriya ya bayyana cewa shirin tallafa wa kare al’ummomin Kiristoci a ƙasar hadin gwiwa ne, ba mataki na kai-tsaye ba
- Ya ce duk wani mataki da Isra’ila za ta ɗauka zai kasance bisa raba bayanan sirri da haɗin kai da gwamnatin Najeriya, tare da mutunta ikon ƙasa
- Jakadan ya jaddada cewa shirin ba Kiristoci kaɗai ya shafa ba, har da Musulmi da sauran ’yan Najeriya da ke fama da matsalar tsaro a yankuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jakadan Isra’ila a Najeriya, Michael Freeman, ya bayyana cewa shirin ƙasarsa na tallafa wa kare Kiristoci a Najeriya ba wani mataki ne na kai-tsaye ba, illa hadin gwiwa da haɗin kai da gwamnatin Najeriya.
Freeman ya ce kalaman Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, kan buɗe wani sabon fagen yaki da tsattsauran ra’ayin addini, na nufin tallafa wa al’ummomin da ake gallazawa a duniya, ciki har da Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan
Israila ta shiga batun muzgunawa Kiristoci a Najeriya, Netanyahu ya fadi shirin da yake yi

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar Arise News, inda ya ce manufar Isra’ila ita ce taimakawa ƙasashen da ke fuskantar barazanar tsaro ta hanyar musayar bayanan sirri, ba tare da keta ikon kowace ƙasa ba.
Manufar Isra’ila kan zuwa Najeriya
Jakadan ya ce Firaminista Netanyahu ya bayyana a sarari cewa Isra’ila na son ganin dukkan al’ummomin da ake gallazawa a duniya sun samu kariya, musamman Kiristoci.
A cewarsa, wannan buri ba ya nufin Isra’ila za ta yi aiki da kanta ba tare da amincewar Najeriya ba. Ya ce maimakon haka, Isra’ila na son yin aiki tare da Najeriya a matsayin abokiya kuma ƙawarta.
Freeman ya ce manufar ita ce tallafa wa kokarin Najeriya wajen dakile rikice-rikice da hare-haren da ke shafar al’ummomi daban-daban, ba tare da nuna banbancin addini ko kabila ba.
Ya ƙara da cewa Isra’ila na ganin matsalar tsaro a Najeriya a matsayin abin da ya shafi kowa, domin hare-haren na shafar Kiristoci, Musulmi da sauran ’yan ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta yi karin haske game da zargin shirin yi wa ƴan adawa ɗauki ɗai ɗai
Yadda Isra'ila za ta yi aiki a Najeriya
Jakada Freeman ya bayyana cewa samar da bayanan sirri ne ginshiƙin duk wata hadin gwiwa da za a yi tsakanin Isra’ila da Najeriya.
Ya ce Isra’ila ba za ta ɗauki wani mataki ba sai da cikakken jagoranci da umarnin hukumomin Najeriya, domin tabbatar da cewa duk abin da ake yi ya dace da dokoki da manufofin ƙasar.
A cewarsa, babu batun daukar mataki kai-tsaye daga Isra’ila, domin duk wani aiki zai kasance bisa shawara da jagorancin gwamnatin Najeriya.

Source: Twitter
Freeman ya ce ba za a bayyana wa jama’a wasu matakan da ake son dauka ba, domin yin hakan na iya lalata manufar tsaro da ake son cimmawa.
Mamdani ya soke dokokin fifita Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa sabon Magajin garin New York, Zohran Mamdani ya soke wasu dokokin da suka fifita Isra'ila a kan wasu kasashe.
Ya bayyana cewa ya soke dokokin ne a birnin New York kamar yadda ya yi alkawari a lokacin yakin neman zaben da ya yi a 2025.
Biyo bayan daukar matakin, Ma'aikatar harkokin wajen kasar Isra'ila ta zargi Mamdani da nuna wariya da ga Yahudawa a duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng