Bayan Kirkiro Masarautu 13, Gwamna Ya Nada Sababbin Hakimai Sama da 140

Bayan Kirkiro Masarautu 13, Gwamna Ya Nada Sababbin Hakimai Sama da 140

  • Gwamnatin jihar Bauchi ya nada sababbin hakimai 142 domin karfafa ayyukan sarakunan gargajiya a fadin masarautu 21
  • Shugaban hukumar kula da harkokin kananan hukumomi ta Bauchi, Abubakar Muhammad Wabi ya ce an rabawa wadanda aka nada takardun kama aiki
  • Ya ce an yi wadannan nade-nade ne bisa tanadin sabuwar dokar masarautun Bauchi ta 2025, ya bukaci hakiman su fifita bukatun al'ummominsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Gwamna Bala Mohammed ya nada mutane 142 a matsayin hakimai a fadin masarautu 21 na Jihar Bauchi.

Ana ganin dai gwamnan ya nada hakiman ne a wani mataki da ya dauka domin karfafa tsarin mulkin gargajiya da tafiyar da al’amuran al’umma a matakin kasa.

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed a fadar gwamnatinsa Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed
Source: Twitter

Gwamnatin Bauchi ta nada hakimai 142

Tribune Nigeria ta rahoto cewa an raba takardun tabbatar nadin mukami ga dukkan wadanda aka nada domin su fara aiki ba tare da wani bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Ana shirin karbar Abba Kabir a APC, Tinubu ya magantu kan salon mulkinsa a Kano

Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi, Abubakar Muhammad Wabi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Bauchi

Abubakar ya yi bayani kan dalilai da kuma ka’idojin doka da suka ba da damar wadannan nade-nade na hakimai a jihar Bauchi.

A cewarsa, an nada hakiman ne bisa Dokar Masarautu ta Jihar Bauchi (Nadi da Tube Sarakuna) ta 2025, wadda ta tanadi tsarin sake fasali da amincewa da masarautun gargajiya a jihar.

Dalilin nada karin hakimai a jihar Bauchi

Abubakar Wabi ya bayyana cewa aiwatar da dokar ya haifar da kirkirar Majalisun Masarautu 21, lamarin da ya sa aka ga bukatar nada sababbin hakimai domin tafiyar da harkokin gundumomi yadda ya kamata.

Ya kara da cewa ana sa ran nadin zai inganta hadin kai tsakanin sarakunan gargajiya da hukumomin gwamnati, musamman a matakin kasa.

Shugaban hukumar ya yaba wa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, bisa jagoranci da goyon bayan da yake bai wa gyare-gyare a tsarin masarautun gargajiya.

Ya kuma gode wa sauran masu ruwa da tsaki bisa hadin kai da suka bayar wajen ganin an aiwatar da dokar masarautu cikin nasara.

Kara karanta wannan

Hadiman Gwamna Abba sun yi matsaya kan sauya shekarsa zuwa APC

Gwamna Bala Mohammed.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Gwamnatin Bauchi ta ja hankalin hakimai

Ya bukaci sababbin hakiman da aka nada da su riko da adalci, gaskiya, daukar nauyi da hidimtawa al’ummominsu, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Abubakar ya jaddada cewa gwamnatin jihar na da kudurin kawo zaman lafiya, hadin kai da ci gaba mai dorewa ta hanyar masarautun gargajiya masu kokarin biyan bukatun jama’a.

Dalilan kirkiro sababbin masarautu 13 a Bauchi

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Bauchi ta share tantamar jama'a kan dalilanta na kafa sababbin masarautu 13 tare da nada sarakuna a jihar.

Sakataren gwamnatin Bauchi, Alhaji Aminu Hammayo ya ce gwamnatin ta yi haka ne domin ƙara haɓaka ci gaban jama’a da kusantar da mulki ga ƙananan hukumomi da al’umma.

A cewarsa, yawan jama’a ya ƙaru ƙwarai, tare da canje-canjen al’adu da ƙarin ƙauyuka da ke buƙatar kulawa ta musamman daga gwamnati, bisa haka aka yanke kara yawan masarautu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262