An Fito da Zarge Zarge kan Wike bayan Ya Fara Rikici da Manyan APC
- ’Yan asalin Babban Birnin Tarayya sun caccaki Ministan Abuja, Nyesom Wike, bisa zargin yin watsi da sarakunan gargajiya da sauran shugabannin al’umma
- Kungiyar AOIYEO ta ce tun hawansa mulki, ministan bai kai wata ziyara ko tattaunawa mai ma’ana da sarakunan gargajiya a birnin tarayya Abuja ba
- AOIYEO ta bayyana cewa irin wannan sakaci ya haifar da ƙorafi da jin an ware ’yan asalin yankin a ƙasarsu, musamman yayin bukukuwa na musamman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - ’Yan asalin Babban Birnin Tarayya (Abuja) a ƙarƙashin kungiyar AOIYEO sun bayyana rashin jin daɗinsu kan abin da suka kira sakacin da Ministan FCT, Nyesom Wike, ke yi wa sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki na yankin.
Shugaban kungiyar, Isaac David, ne ya bayyana wannan matsaya a madadin ’yan asalin yankin yayin wani taron manema labarai da aka gudanar.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto ya ce damuwar tasu ta samo asali ne daga yadda ministan ke mu’amala da shugabannin gargajiya a wasu jihohi, amma ya yi biris da na Abuja.
Korafin 'yan Abuja kan Nyesom Wike
Isaac David ya nemi jin dalilin da ya sa Nyesom Wike ya samu lokacin ziyartar sarakunan gargajiya a ƙananan hukumomin Jihar Rivers, amma tun hawansa matsayin Ministan FCT bai kai ko ziyara ɗaya ga sarakunan gargajiya a yankin ba.
Ya ce tun daga lokacin da aka naɗa shi, ministan bai ziyarci ko fada ɗaya ba a Abuja, kuma bai gudanar da wata tattaunawa mai ma’ana da dattawa, shugabannin matasa ko ƙungiyoyin mata a ƙananan hukumomi shida na yankin ba.
A cewarsa, wannan abin takaici ne domin sarakunan gargajiya da sauran shugabannin al’umma su ne ginshiƙan mulki a matakin ƙasa, kuma su ne ke da rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan jama’a.
Zargin da aka yi wa Wike kan sarakuna
Shugaban AOIYEO ya jaddada cewa sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki na al’umma su ne ke bayar da shawarwari da goyon baya da ake buƙata domin kyakkyawan shugabanci da ci gaban al’umma.
Ya ce watsi da su na nufin watsi da muradin jama’a, lamarin da ke iya kawo cikas ga aiwatar da manufofi da shirye-shiryen raya ƙasa.
A cewarsa, irin wannan hali ya nuna kamar ministan bai ba da muhimmanci ga gudummawar da shugabannin gargajiya ke bayarwa ba.
David ya ƙara da cewa sakacin ya haifar da ɓacin rai da jin an nuna wariya a tsakanin ’yan asalin yankin da mazauna birnin tarayyar, waɗanda ke ganin kamar an mayar da su saniyar ware a ƙasarsu ta gado.
Wike ya bar Abuja, ya tafi Rivers
Shugaban kungiyar ya kuma soki matakin ministan na shafe lokutan bukukuwa yana ziyartar sarakunan gargajiya a wasu jihohi, maimakon kula da shugabancin gargajiya a yankin da yake jagoranta.
Ya ce a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, sarakunan gargajiya da mazauna ƙananan hukumomi shida na Abuja sun jira ko da gayyata ko ganawa, amma hakan bai faru ba.

Source: Facebook
A cewarsa, wannan hali ya tayar da tambayoyi masu nauyi kan ko ministan na ɗaukar ’yan asalin Abuja da muhimmanci ne kawai a lokacin zaɓe, ko kuma idan bukatun siyasa suka taso.
Sakataren APC na rikici da Wike
A wani labarin, kun ji cewa Sakataren jam'iyyar APC na kasa, Sanata Ajibola Basiru ya bukaci Nyesom Wike ya ajiye mukamin ministan Abuja.
Sanata Basiru ya fadi haka ne yayin da ya ke magana a kan yadda Wike ke tsoma baki a harkokin jihar Rivers, musamman a kan APC.
Sakataren APC ya kara da cewa ministan Abuja ba dan APC ba ne, saboda haka bai kamata ya rika saka baki a lamuran jam'iyyar ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


