Kwankwaso Ya Fito da Abubuwan Alheri da Ya Yi wa Abba Kabir a Baya
- Rabiu Musa Kwankwaso ya taya Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, murnar zagayowar ranar haihuwarsa tare da tuno da doguwar tafiyar siyasar da suka yi tare
- Saƙon na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin sauya sheƙar siyasa, inda ake hasashen Abba Kabir Yusuf na shirin ficewa daga jam'iyyar NNPP zuwa APC
- Sai dai duk da maganganun da ake yi, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai fito karara ya yi magana a kan sauya shekar ba a sakon taya murna da ya turawa gwamnan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya aike da saƙon taya murnar zagayowar ranar haihuwar Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Saƙon na Kwankwaso ya zo ne a wani yanayi na siyasa da ake ta rade-radi game da makomar dangantakar siyasa tsakaninsa da Abba, musamman ma ganin jita-jitar cewa gwamnan na duba yiwuwar sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC.

Source: Twitter
A cikin saƙon da ya wallafa a Facebook, Kwankwaso ya mayar da hankali kan tarihinsu na aiki tare, yana bayyana irin rawar da Abba ya taka a tsare-tsaren da suka aiwatar domin ci gaban Jihar Kano.
Alheran da Kwankwaso ya yi wa Abba
A saƙon taya murnar, Kwankwaso ya ce ya yi amfani da ranar ne domin tunawa da shekarun da suka shafe suna tafiya tare a siyasa, inda Abba ya riƙe muhimman mukamai a ƙarƙashinsa.
Ya bayyana cewa a zangonsa na farko a matsayin gwamnan Kano, Abba ya fara aiki a matsayinsa na mataimaki na musamman, inda daga bisani ya cigaba da zama PA a lokacin da Kwankwaso ya riƙe mukamin minista.
Kwankwaso ya ƙara da cewa a zangonsa na biyu, Abba ya yi aiki a matsayin PPS, sannan daga baya ya zama kwamishina, mukaman da ya ce sun ba da gudummawa wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da suka assasa don ci gaban jihar.
A ƙarshen saƙon, Kwankwaso ya yi addu’ar Allah Ya ba Abba hikima da lafiya a rayuwarsa, yana mai jaddada irin rawar da ya taka har zuwa zama gwamnan Kano a halin yanzu.
Taron cika shekara 63 da haihuwar Abba
Mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa bikin zagayowar ranar haihuwar Abba Kabir Yusuf ya gudana a Kano.
A sakon da ya wallafa a Facebook, Sanusi Bature ya ce an shirya wani ƙaramin taro na sirri da dangi suka gudanar, inda shi da Hon. Abdullahi Rogo suka kasance tare da gwamnan a wajen bikin.

Source: Facebook
Tinubu ya taya Abba Kabir murna
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ma ya aike da saƙon taya murna ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, a zagayowar cikarsa shekaru 63.
A cikin saƙon, shugaban ƙasar ya yabawa Abba bisa gaskiya, tawali’u, halayen da ya ce suna bayyana a yadda yake tafiyar da al’amuran mulki a Kano.
Ya bayyana cewa mulkin Abba Kabir Yusuf a Kano, wadda ya kira cibiyar siyasar Arewa, na nuna jajircewa wajen bunƙasa rayuwar talakawa, bisa tafarkin da marigayi Malam Aminu Kano ya assasa a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

