Kotu Ta Tabbatar da Hukuncin Kisa kan Farida, Matar da Ta Kashe Tsohon Mijinta

Kotu Ta Tabbatar da Hukuncin Kisa kan Farida, Matar da Ta Kashe Tsohon Mijinta

  • Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan Farida Abubakar saboda kashe tsohon mijinta a jihar Kebbi
  • Masu gabatar da kara sun nuna cewa Farida ta daba wa marigayin, tsohon babban majistare wuka saboda yana shirin kara aure
  • Farida Abubakar ta daukaka kara zuwa Kotun Koli ta kasa domin neman soke wannan hukunci bayan kotuna biyu sun same ta da laifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zama a Sokoto ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke wa Farida Abubakar, sakamakon samun ta da laifin kisan tsohon mijinta, shugaban alkalan kotunan majistare, Attahiru Muhammad-Ibrahim.

A wani hukunci na bai-ɗaya da aka yanke a ranar Litinin, kwamitin alƙalai uku ƙarƙashin Mai shari’a Tunde Awotoye, ya yi watsi da ƙarar da Farida ta shigar.

Kara karanta wannan

Babbar kotun tarayya ta shirya zama kan bukatar da Abubakar Malami ya shigar gabanta

Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kisa kan Farida, matar da ta kashe tsohon mijinta a Kebbi
Alkalai na zaune yayin da ake gudanar da zaman shari'a a kotun daukaka kara, Abuja. Hoto: @NGCourtofAppeal
Source: Twitter

An tabbatar da hukuncin kisa kan Farida

Mai shari'a Tunde Awotoye ya ce kwamitin alkalan ya kuma amince da hukuncin Babbar Kotun jihar Kebbi na ranar 3 ga watan Yuni, 2024, cewar rahoton Punch.

Kotun ta bayyana cewa masu shigar da ƙara sun tabbatar da laifin Farida fiye da shakku, inda suka dogara da shaidun gani da ido da kuma dabarar shari’a ta "wanda aka gani ƙarshe".

Bincike ya nuna cewa Farida ce ta ƙarshe da aka gani tare da marigayin a gidansa da ke Birnin Kebbi kafin a tsinci gawar sa.

Kotun ta tabbatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a ƙarƙashin sashe na 191(b) na dokar jihar Kebbi, da kuma zaman gidan yari na shekaru bakwai saboda raunata marigayin.

Yadda aka kashe Majistare Attahiru

A lokacin shari’ar, masu shigar da ƙara sun gabatar da shaidu 12 da kuma wasu muhimman hujjoji, ciki har da Hijabin Farida wanda ke dauke da jini a jikinsa.

Kara karanta wannan

Tsohuwar ministar Buhari ta faɗi waɗanda suka yi kutun kutun ta rasa kujerarta

Shaidun sun nuna cewa Farida ta yi amfani da wani abu mai kaifi ta daba wa alkalin a cikinsa, wuyansa, da kuma hannunsa na hagu, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

Mai shari'a Tunde Awotoye ya bayyana cewa Farida ta shirya wannan harin ne da gangan, a daidai lokacin da marigayin ke shirin ƙara aure.

An ce Farida ta kashe tsohon mijinta da wani abu mai kaifi saboda yana shirin kara aure.
Taswirar jihar Kebbi, inda Farida ta kashe tsohon mijinta, shugaban alkalan kotun Majistare. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Farida ta daukaka kara zuwa Kotun Koli

Duk da tabbatar da wannan hukunci da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi, Farida Abubakar ba ta amince ba, inda tuni ta shigar da ƙarin neman ɗaukaka ƙara a gaban Kotun Ƙoli.

Rahoto ya nuna cewa, Farida tana fatan Kotun Ƙolin za ta soke hukuncin kotunan biyu na baya domin ta tsira daga hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Wannan shari’a dai ta ja hankalin jama’a sosai tun bayan aukuwar lamarin a watan Agusta na shekarar 2022, kuma masana na ganin gaskiya ce ta yi halinta a kotunan biyu.

Uwargida ta 'kashe' mijinta saboda kishiya

A wani labari, mun ruwaito cewa, ana zargin wata mata mai suna Favour Odoba ta kashe mijinta, Abdul-Kadir Nagazi, a garin Okene da ke Jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Abun ya yi muni: 'Yan bindiga sun kai mummunan hari Kebbi, an rasa rayuka

Majiyoyi sun bayyana cewa ma’auratan sun shafe kusan shekara tara da aure amma Allah bai nufa sun samu karuwa ta ɗa ba, lamarin da ya sanya shi karo aure.

Rikici ya fara ne bayan mijin ya auri wata mata ta biyu wadda ta haifo masa magaji, inda Favour ta hau dokin zuciya, ta aika mijinta lahira ta hanyar sanya guba a abincinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com