Jami'an Tsaro Sun Fafata da 'Yan Bindiga, an Ceto Mutanen da Aka Sace a Zamfara
- 'Yan bindiga sun kutsa zuwa kauyen Dunfawa na karamar hukumar Moriki ta jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da bayin Allah da dama
- Jami'an tsaro sun kai daukin gaggawa inda suka yi artabu da tsagerun 'yan bindigan, inda hakan ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji
- Biyo bayan ragargazar 'yan bindigan da jami'an tsaron suka yi, an samu nasarar ceto dukkanin mutanen da aka yi garkuwa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - An samu nasarar ceto dukkan mutane 20 da aka sace daga kauyen Dunfawa da ke yankin Moriki, a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an ceto mutanen ne bayan 'yan bindiga sun sace su.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
An sace mutanen ne tun da sanyin safiyar ranar Asabar, 3 ga watan Janairun 2026 bayan wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kauyen, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin tsoro da firgici.
Yadda aka ceto mutanen Zamfara da aka sace
Majiyoyi sun bayyana cewa an samu nasarar ceto mutanen ne da misalin karfe 4:00 na yamma, sakamakon matsin lamba mai tsanani da jami’an tsaro na hadin gwiwa suka yi wa 'yan bindiga a yankin Moriki.
A cewar majiyoyin, aikin ceton ya samu nasara ne bayan hadin kai da tsare-tsaren jami’an tsaro da aka tura yankin, wanda ya tilasta wa ‘yan bindigan barin mutanen da suka sace sannan suka tsere.
“An ceto dukkan mutanen 20 cikin koshin lafiya ba tare da wani rauni ba. An kai su asibitin gwamnati domin duba lafiyarsu, daga bisani aka yi musu tambayoyi kafin a mika su ga iyalansu."
- Wata majiya
Jami'an tsaro na ci gaba da sintiri
Sun kara da cewa an kara kaimi wajen sintiri na hadin gwiwa a yankin, domin hana sake aukuwar hare-hare tare da taimakawa wajen yiwuwar ceto wasu da aka sace a kauyuka makwabta.
Mazauna kauyen Dunfawa sun bayyana jin dadinsu bisa samun nasarar ceton mutanen, tare da rokon hukumomi da su ci gaba da tsaurara tsaro domin hana sake faruwar sace-sace a gaba.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- Yadda 'yan bindiga suka kashe mutum 60 a kasuwar Neja ana hada-hada
- 'Yan bindiga sun kai hari kan shingen binciken NSCDC, sun bude wa jami'ai wuta
- Daliban Neja sun fadi halin da suka shiga hannun 'yan bindiga bayan shakar iskar 'yanci
'Yan ta'adda sun farmaki 'yan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'adda dauke da makamai sun kai hari kan wani shingen binciken 'yan sanda a jihar Neja.
Yan ta'addan wadanda suka zo kan babura, sun kai harin ne a kauyen New Kalli da ke karamar hukumar Borgu a jihar Neja.
Maharan sun kona masaukin jami’an tsaro, suka lalata amfanin gona na manoma tare da kwashe wasu kayayyakin kafin su tsere.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

