An Rufe Matatar Dangote Ta Daina Aiki Gaba Daya a Najeriya? Bayanai Sun Fito

An Rufe Matatar Dangote Ta Daina Aiki Gaba Daya a Najeriya? Bayanai Sun Fito

  • Jita-jitar da ake yadawa cewa matatar hamshakin dan kasuwar nan, Aliko Dangote ta daina aiki domin yin gyara ba gaskiya ba ne
  • Matatar Dangote ta karyata labarin, tana mai cewa aikin tace mai na ci gaba da tafiya yadda ya kamata domin wadatar da fetur ga 'yan Najeriya
  • Ta kuma jaddada cewa har yanzu farashin kowace litar fetur a rumbunan a ajiyar da take cinikayya da 'yan kasuwa, na nan a N699

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Matatar mai ta Dangote da ke jihar Legas ta musanta labarin da ake yadawa cewa ta dakatar da ayyukanta na dan lokaci domin yin wasu gyare-gyare.

Matatar Dangote ta karyata rahoton, wanda wasu ke yada cewa tana shirin rufewa domin aikin gyara, inda ta bayyana labarin a matsayin ƙarya da yaudara.

Kara karanta wannan

Yadda gobara ta tashi a kasuwar Sakkwato, ta shafe shaguna sama da 40

Dangote.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da rumbun ajiyar matatarsa Hoto: Dangote Group
Source: Getty Images

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rukunin kamfanonin Dangote Group, wanda ya kunshi matatar mai, ya fitar a shafinsa na X a ranar Litinin.

An rufe Matatar Dangote na dan lokaci?

Matatar ta jaddada cewa ayyukan samar da mai na ci gaba da gudana yadda ya kamata, cikin kwanciyar hankali kuma ba tare da katsewa ba.

“Matatar Dangote na aiki, kuma tana da ƙarfin samar da lita miliyan 40 zuwa 50 na fetur a kullum a watannin Janairu da Fabrairu, gwargwadon buƙatar kasuwa." in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa a ranar 4 ga Janairu 2025, matatar ta samar da lita miliyan 50 na fetur kuma ta fitar da lita miliyan 48 zuwa rumbunanta na kasuwanci.

“Adadin man da muke da shi a ajiye a halin yanzu ya isa wadatar da 'yan kasa na tsawon kwanaki 20, wanda hakan na kara kawo natsuwa da kawar da duk wani fargabar ƙarancin mai.”

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun yi magana da murya daya kan harin da aka kai kasuwar Neja

Matatar Dangote ta tabbatar da rage farashi

Bugu da kari, matatar Dangote ta jaddada cewa farashin kowace litar man feturinta na nan a N699 ga 'yan kasuwa da masu saye kadan-kadan a fadin Najeriya.

Ta bukaci gidajen mai, manyan kamfanoni da cibiyoyi da su dawo amfani da man da ake tacewa a cikin gida, wanda ya fi araha, tsabta kuma mai inganci, maimakon dogaro da wanda ake shigo da shi daga waje.

Aliko Dangote.
Shugaban kamfaninin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote Hoto: @Dangitegroup
Source: Getty Images
“Ta hanyar sayen fetur a cikin gida kan N699/lita, ‘yan kasuwa za su iya rage farashi ga yan Najeriya, su tabbatar da daidaiton kasuwa, sannan su tallafa wa shirin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya,” in ji matatar.

A cewar matatar Dangote, ba don feturin da ake tacewa a cikin gida ba, da farashin fetur zai iya haura N1,400 kan kowace lita bayan cire tallafi, in ji Premium Times.

NNPCL ya rage farashin fetur a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin NNPCL ya sanar da sake rage farashin litar man fetur da N20 a gidajen mansa, matakin da zai shafi masu saye da sayarwa a kasar nan.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Likitoci sun sanya ranar da za su koma yajin aiki a fadin Najeriya

Binciken da aka gudanar a wasu gidajen mai na NNPC a birnin tarayya Abuja ya nuna cewa yanzu ana sayar da litar man fetur a kan N815, maimakon N835 da ake sayarwa a baya.

Majiyoyi daga cikin kamfanin sun bayyana cewa sauke farashin ya biyo bayan wani umarni na cikin gida da aka amince da shi a daren Lahadi, 4 ga Janairun 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262