Kwana Ya Kare: Tsohon Sanata Ya Rasu a Abuja, Gwamna Ya Shiga Damuwa
- An tabbatar da rasuwar tsohon sanatan da ya wakilci Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, John Kojo-Brambaifa a wani asibiti a Abuja
- Gwamna Douye Diri ya nuna damuwarsa da alhini bisa rasuwar tsohon sanatan, wanda ya bayyana da jajirtaccen mutum wanda ya taimaki jama'a
- A madadin gwamnati da al'ummar Bayelsa, Gwamna Diri ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da sauran al'ummar kauyen Agbere
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bayelsa, Nigeria - Najeriya ta kara rasa daya daga cikin tsofaffin sanatoci da suka ba da gudummuwa wajen yi wa jama'a hidima.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon sanata daga jihar Bayelsa, John Kojo-Brambaifa ya riga mu gidan gaskiya.

Source: Facebook
Tsohon Sanata daga Bayelsa ya rasu
Premium Times ta ce Marigayi Brambaifa, wanda ya wakilci mazabar Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya ta biyar ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin tarayya Abuja.
Bayanai sun nuna cewa tsohon sanata ya mutu yana da shekaru 81 a duniya bayan fama da rashin lafiya.
Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon sanatan, inda ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen ɗan siyasa wanda ya nuna kwarewa da nagarta a hidimar jama’a.
Gwamna Diri ya yi alhinin rasuwar Brambaifa
“Bayelsa da Najeriya sun rasa dattijo mai daraja, mutumin kirki, gogaggen ɗan siyasa kuma babban jagoran al’umma.
“Brambaifa ya bar tarihin hidima mai tsabta da jajircewa ga ci gaban Najeriya, tsohuwar Jihar Ribas, Bayelsa da kuma al’ummarsa baki ɗaya."
- In ji Gwamna Douye Diri.
Gwamna Diri ya bayyana hakan ne a cikin sakon ta’aziyya da Babban Sakataren Yada Labaransa, Daniel Alabrah, ya fitar ranar Litinin, 5 ga watan Janairu, 2025.
Gwamnatin Bayelsa ta mika sakon ta'aziyya
“A madadin gwamnatin Jihar Bayelsa, ina mika ta’aziyya ga iyalan Brambaifa da al’ummar Agbere da ke Karamar Hukumar Sagbama, inda ya fito,” in ji Diri.
Gwamnan ya bukaci iyalan marigayin da al’ummarsa da su samu nutsuwa da kwarin gwiwa bisa la’akari da kyakkyawan aiki da gagarumar rawar da ya taka a harkokin siyasa da mulki.

Kara karanta wannan
Lokaci ya yi: An dawo da gawar Sanata Najeriya bayan Allah ya masa rasuwa a Indiya

Source: Twitter
Takaitaccen bayani game da marigayi Brambaifa
Kafin rasuwarsa, Sanata Brambaifa shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Noma ta Tarayya da ke Bassambiri, a Karamar Hukumar Nembe ta Jihar Bayelsa, in ji Daily Post.
Haka kuma, ya taba zama Shugaban Karamar Hukumar Sagbama a tsohuwar Jihar Ribas, sannan ya taba rike mukamin Shugaban Hukumar Haraji ta Jihar Bayelsa.
Gawar Sanata Godiya Akwashiki ta iso Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gawar sanatan Nasarawa ta Arewa, Godiya Akwashiki ta iso Najeriya daga kasar Indiya bayan Allah ya karbi ransa a asibitin da ya yi jinya.
Wata majiya daga iyalansa, wadda ta yi magana bisa sharadin sakaya sunanta saboda ba ta da izinin hira da kafafen watsa labarai, ta tabbatar da dawo da gawar sanatan gida Najeriya.
Majiyar ta ce abokan siyasar sanatan, shugabannin jam’iyyar SDP da magoya baya ne suka tarbi gawar, ciki har da tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Al-Makura.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
