Yadda Gobara Ta Tashi a Kasuwar Sakkwato, Ta Shafe Shaguna sama da 40
- Wata mummunar gobara da ta tashi a Garejin Buzaye da ke jihar Sakkwato, ta cinye shaguna da motoci da dama da jefa jama'a a fargaba
- Ana zargin matsalar lantarki ce ta haddasa gobarar da ta yi ta barna na tsawon sa’o’i kafin a yi nasarar shawo kanta
- Masu sana’a da suka bayyana halin da suke ciki sun nemi gwamnatin jihar ta kawo musu ɗauki bayan asarar da suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Wata mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar kayan gyaran motoci da ake kira Garejin Buzaye a Jihar Sakkwato, inda yi ɓarna mai waya.
Rahotanni sun bayyana cewa wutar da ta shafe sa'o'i tana ci ta lalata shaguna da motoci da kadarori masu yawa, tare da jefa ƴan kasuwa a halin Ni ƴasu.

Source: Original
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa lamarin ya faru ne da misalin 10:00 na safiyar Litinin, abin da ya jefa ’yan kasuwa da masu sana’a cikin firgici da alhini.
Gobara ta cinye kadarori a kasuwar Sakkwato
Daily Post ta wallafa cewa rahotanni daga wurin sun nuna cewa wutar ta bazu cikin sauri saboda yawan kayan da ke kamawa da wuta a yankin, ciki har da mai, gas da kayayyakin walda.
Wani mai gyaran mota ya shaida mana cewa akalla shaguna 40 ne suka ƙone, tare da wuraren gyaran motoci irin su na marsandi da kuma shagunan sayar da sassan motoci.
Wasu daga cikin motocin da suka ƙone mallakin ’yan Sakkwato ne, yayin da wasu kuma suka fito ne daga Jamhuriyar Nijar.

Source: Facebook
A lokacin da ake tattara wannan rahoto, jami’an kashe gobara na ci gaba da aiki domin shawo kan wutar, tare da taimakon mazauna yankin.
Shaidu sun ce wutar ta dauki lokaci kafin a iya rage ta, saboda karancin kayan aiki da kuma yanayin kasuwar da ke cike da abubuwan haɗari.
Kanikawa a Sakkwato sun nemi ɗauki
Shugaban Ƙungiyar Kanikawa ta Najeriya (NATA), reshen Garejin Buzaye, Injiniya Abdulkadir Muhammad, ya bayyana lamarin a matsayin abin tausayi.
Ya ce har yanzu ba a iya tantance adadin ainihin asarar ba, domin gobarar na ci gaba da cinye wasu sassa a lokacin da yake magana.
Injiniya Muhammad ya danganta tashin gobarar da matsalar lantarki, yana mai cewa cunkoson kayan mai da gas a wurin ya ƙara tsananta wutar.
Ya yi kira ga gwamnatin Jihar Sakkwato da ta kawo agaji ga ’yan kasuwar da abin ya shafa, duba da cewa da dama daga cikinsu sun rasa tushen abincinsu gaba ɗaya.
An samu bayanai kan harin Sakkwato
A baya, mun wallafa cewa babbar hedkwatar sojojin kasa (DHQ) ta sake tabbatar da cewa farmakin da Amurka ta jagoranta a Jihar Sakkwato ya yi tasiri sosai, tare da daƙile harin ƴan ta'adda.
Hedkwatar sojojin Najeriya ta bayyana cewa an kai harin ne bisa sahihan bayanan sirri da aka tattara tun da wuri, lamarin da ya taimaka wajen cimma gagarumar nasara a kan sansanonin ’yan ta’adda.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na DHQ, Manjo Janar Michael Onoja, ya yi wa manema labarai a Abuja, ya ce ana ci gaba da tantance irin barnar da farmakin ya jawo wa ’yan ta’addan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


