Ana Ta Tambayoyi bayan Hango Tambarin Grok a Hoton Tinubu a Faransa

Ana Ta Tambayoyi bayan Hango Tambarin Grok a Hoton Tinubu a Faransa

  • Wani hoto da aka wallafa daga ganawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shugaban Rwanda, Paul Kagame, ya jawo ce-ce-ku-ce bayan an lura da tambarin Grok a jikinsa
  • Masu amfani da kafar X sun fara tambayar sahihancin hoton, suna nuna damuwa kan dalilin amfani da hoto mai tambarin fasahar kirkirar hotuna ta AI
  • Lamarin ya ƙara ɗaukar hankali ne bayan hadimin shugaban kasa kan kafafen sada zumunta ya sake wallafa hoton, abin da ya haifar da rade-radi a tsakanin 'yan kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Faransa - Hoton da aka ce daga ganawar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi da shugaban Rwanda, Paul Kagame, a birnin Paris ya haifar da muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta, bayan an lura da tambarin Grok a kansa.

Kara karanta wannan

Bayan shirin barin Kwankwaso, da gaske Abba Kabir zai tarbi Aminu Ado Bayero?

An ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya gana da Kagame ne a birnin Paris na Faransa, inda aka ce ganawar ta shafi batutuwan diflomasiyya.

Hoton Bola Tinubu da Paul Kagame
Hoton shugaba Bola Tinubu mai tambarin Grok. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Hoton ya bayyana ne a shafin shugaba Tinubu a kafar X, inda masu amfani da dandalin suka hango tambarin Grok, wata manhajar kirkirar bayanai da hotuna ta hanyar fasahar AI.

Hoton Tinubu da Grok ya tada kura

Grok wata manhaja ce ta fasahar kirkirar bayanai da hotuna da kamfanin xAI mallakin Elon Musk ya ƙirƙira. Ana saninta da iya bincike kai tsaye da kuma samar da hotuna ta hanyar fasaha.

Masu amfani da kafar X sun nuna mamaki kan yadda hoton ganawar shugabanni biyu ya ɗauki tambarin Grok, abin da ya sa wasu suka fara tambayar ko hoton na asali ne ko kuma an samar da shi ta hanyar fasahar AI.

Halin ya ƙara ɗaukar hankali ne bayan mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ya sake wallafa hoton, lamarin da ya ƙara rura wutar muhawara a intanet.

Martanin masu amfani da kafar X

Kara karanta wannan

Trump ya jefa bama bamai a Venezuela, ya cafke shugaban kasa Maduro da matarsa

Punch ta wallafa cewa masu amfani da kafar X da dama sun yi suka kan wallafa hoton, suna tambayar dalilin da ya sa aka yi amfani da hoto mai tambarin fasahar AI wajen nuna wani muhimmin taron diflomasiyya.

Wani mai amfani da X mai suna Olayinka, wanda ke amfani da sunan @mickoly, ya rubuta cewa:

“A ina Tinubu yake a Turai? Me ya sa aka wallafa hoton da Grok ya ƙirƙira? Shin babu hoton gaske daga ganawar?”

Wani mai suna Joshua Siyanbola, @JoshuaSiyanbol4, ya ce hoton yana kama da wanda aka samar ta hanyar fasahar AI, yana mai cewa yana ɗauke da tambarin Grok, kuma ya yi imanin cewa ya kamata a yi abin da ya fi haka.

Fadar shugaban kasa ta yi bayani

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya yi karin bayani game da hoton, inda ya ce da wayar hannu aka dauke shi.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Bayo Onanuga ya ce an yi amfani da fasahar Grok ne wajen gyara kyawun hoton kawai, ba abin da wasu ke tunani ba.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ana zargin Tinubu zai sauya sunan Najeriya

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawo shirin tallafi na 2026, talakawa miliyan 10 za su amfana

A wani labarin, mun kawo muku cewa wani fasto mai suna Toye Ebijomore ya fitar da hasashen abubuwan da za su faru a Najeriya a 2026.

Faston ya yi ikirarin cewa shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu, zai sauya sunan kasar kafin ya kammala wa'adin mulkinsa.

Ya kuma yi hasashen cewa za a samu yalwar abinci a Najeriya a 2026, sai dai kuma matsalolin tsaro za su sauya salo a fadin kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng