Yadda Wasu Kananan Yara Suka Gano Harsasan Kakkabo Jiragen Sama a Borno

Yadda Wasu Kananan Yara Suka Gano Harsasan Kakkabo Jiragen Sama a Borno

  • Wasu kananan yara sun tsinci tarin harsasan kakkabo jiragen sama a wata magudanar ruwa a yankin Bulunkutu na jihar Borno
  • Mazauna yankin sun yi zargin cewa 'yan Boko Haram ne suka bar waɗannan makaman kafin a kore su daga yankin a shekarun baya
  • A cikin wani faifan bidiyo, an ga jami'an tsaro suna karrama yaran da suka tsinci harsasan, saboda nuna jarumtaka da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Wasu ƙananan yara da suka tafi kamun kifi a wata magudanar ruwa sun tsinci tarin harsasan kakkabo jiragen sama a Borno.

Yara 11 ne suka tsinci harsasan, inda babbansu ke da shekaru 13 kacal, lamarin da ya jefa mutanen yankin Bulunkutu da ke birnin Maiduguri a firgici.

Kananan yara sun tsinci harsasan kakkabo jiragen sama a Borno.
Dakarun sojojin Najeriya a lokacin da suke sintiri da tarin alburusan da aka gano a Borno. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Yara sun tsinci harsasan harbo jirgi a Borno

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun yi magana da murya daya kan harin da aka kai kasuwar Neja

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa, maimakon yaran su kamo kifi kamar yadda suka saba a duk lokacin da ruwa ya fara ja baya, sai komarsu ta kamo tarin harsasai da na'urorin cajin waya waɗanda aka ɓoye a cikin magudanar ruwan.

Ganin waɗannan abubuwa da ba su saba gani ba ya sa yaran suka sanar da manya, waɗanda su kuma suka kira jami'an tsaro.

Rundunar sojoji ta Operation Hadin Kai, tare da haɗin gwiwar 'yan sanda da dakarun sa-kai na CJTF, sun garzaya wurin tare da killace yankin baki ɗaya.

Malam Bishir, wani mazaunin yankin, ya bayyana cewa mutane na zargin cewa 'yan Boko Haram ne suka bar waɗannan makaman kafin a fatattake su daga yankin a shekarun baya.

An bayyana kalar harsasan da aka gano

Jaridar The Cable ta rahoto cewa jami'an tsaro sun gano aƙalla harsasai guda 1,270 masu kirar 12.7mm a daidai yankin layin dogo na Bulunkutu.

Jami'an kwance bama-bamai na 'yan sanda (EOD) sun bincika magudanar ruwan sosai domin tabbatar da cewa babu sauran abubuwan fashewa da aka ɓoye.

Wannan nasara ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara tsaurara tsaro a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa sakamakon hare-haren ƙunar-baƙin-wake da aka samu a makonnin baya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi dirar mikiya a kasuwa, an rasa rayukan mutane da dama a Neja

An karrama yaran da suka tsinci harsasai a magudanar ruwa a Borno
Taswirar jihar Borno, inda kananan yara suka tsinci harsasai a magudanar ruwa. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An karrama yaran da suka tsinci harsasan

A wani faifan bidiyo da aka gani, an ga yaran su 11 a zaune yayin da jami'an tsaro na Sector 9 ke yaba musu tare da ba su kyautar kuɗi saboda bajintar da suka nuna na rashin wasa da waɗannan kayan yaƙi.

Jami'an tsaro sun tabbatar wa mazauna yankin cewa za su ci gaba da kasancewa a wurin domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, tare da hana ɓata-garin da suka ɓoye makaman sake dawowa yankin.

Bam ya tarwatse da yara a Borno

A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar ‘yan sanda ta ce yara hudu sun mutu bayan fashewar wani bam da aka ce yaran sun dauko daga cikin bola.

Rundunar 'yan sandan ta rahoto cewa wani yaro dan shekara 12, Mustapha Tijja ya samu munanan raunuka kuma an kai shi asibitin FHI 360 NGO a Banki.

Kwamishinan ‘yan sandan Borno, CP Naziru Abdulmajid ya yi gargadi ga jama’a musamman yara da su guji wasa da abubuwan da ba su saba gani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com