Da Gaske Amurka Ta Yi Shirin Kashe Sheikh Gumi? Malamin Ya Magantu
- Sheikh Ahmad Gumi ya ce bai taɓa faɗin cewa hare-haren jiragen yaƙin Amurka a Sokoto sun yi niyyar kawar da shi ba, yana mai cewa abin da ke yawo tsohon bidiyo ne da aka karkatar
- Malamin ya bayyana cewa kalamansa da ake yadawa sun shafi barazanar da Boko Haram suka yi masa a shekarar 2012, ba wai wata barazana ba ce da ke da alaƙa da hare-haren Amurka
- Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai da suka ruwaito labarin da ba daidai ba su janye shi tare da bayar da haƙuri, yana jaddada cewa rayuwarsa tana cikin kwanciyar hankali a halin yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya fito fili ya karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa harin Amurka a Sokoto sun yi niyyar kawar da shi.
Sheikh Gumi ya ce labarin ya samo asali ne daga wani tsohon bidiyo da aka fassara ba daidai ba, inda aka danganta shi da sabon yanayi duk da cewa maganarsa ta shafi wani abu da ya faru shekaru da dama da suka wuce.

Source: Facebook
Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne a sako da ya fitar a shafinsa na Facebook, inda ya tabbatar da cewa babu wata barazana ga rayuwarsa a yanzu, sabanin rade-radin da ke yawo.
Da gaske Amurka za ta kashe Ahmad Gumi?
Sheikh Ahmad Gumi ya ce abin da ke yawo a kafafen sadarwa labari ne na ƙarya da aka gina kan kuskuren fahimtar tsohon wa’azi da ya yi.
Malamin ya tabbatarwa Leadership cewa bai taɓa cewa Amurka ta yi niyyar kawar da shi ta hanyar hare-haren jiragen yaƙi a Najeriya ba.
A cewarsa, wasu 'yan jarida sun ɗauki maganarsa sun karkatar da ita, inda suka haɗa ta da hare-haren da Amurka ta kai kan ’yan ta’adda a jihar Sokoto.
Sheikh Gumi ya ce yana zaune lafiya a gidansa tare da iyalansa, ba tare da tsoro ko fargaba ba, yana mai cewa babu wata barazana da ke fuskantar rayuwarsa a halin yanzu.
Asalin barazanar da aka yi wa Gumi
Malamin ya bayyana cewa asalin maganar da ake yadawa ta shafi wani lamari ne da ya faru a watan Agusta na shekarar 2012, lokacin da aka sanar da shi cewa ƙungiyar Boko Haram ta shirya kawar da shi.
Ya ce a wancan lokaci, wasu mutane biyu da aka ce an turo domin aiwatar da shirin sun mutu a nan take lokacin da bam ɗin da suke ɗauke da shi ya tarwatse a hannunsu kusa da gidansa.

Source: UGC
Sheikh Gumi ya ce wannan lamari ne da ya riga ya wuce, kuma ya yi imanin cewa Allah Madaukakin Sarki ne Ya tsare shi daga waɗanda suka ɓoye kansu da sunan Boko Haram a wancan lokaci.
Kiran Gumi ga kafafen yaɗa labarai
Sheikh Gumi ya nuna damuwa kan yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka ɗauki labarin ba tare da tantance gaskiyarsa ba. Ya ce hakan ya jefa jama’a cikin ruɗani tare da haifar da tsoro da ba shi da tushe.
Ya buƙaci duk wata kafar labarai da ta wallafa ko ta yaɗa rahoton da ba daidai ba ta fito fili ta janye shi tare da bayar da haƙuri ga jama’a.
Gumi ya maka mutum 2 a kotu
A wani labarin, kun ji cewa malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya maka wasu mutane biyu a kotu.
Malamin ya dauki matakin ne bayan mutanen sun wallafa wasu sakonni a kafar Facebook suka jingina masa ba tare da ya fadi abin da ake cikin sokon ba.
Sakon da ke cikin abin da suka rubuta ya kunshi gargadi ga ministan tsaro, Janar Christopher Musa (Mai ritaya) game da yakar 'yan bindiga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


