Ana Shirin Karbar Abba Kabir a APC, Tinubu Ya Magantu kan Salon Mulkinsa a Kano

Ana Shirin Karbar Abba Kabir a APC, Tinubu Ya Magantu kan Salon Mulkinsa a Kano

  • Shugaba Bola Tinubu ya yabawa salon mulkin Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf duba da ayyukan ci gaba da ya samar
  • Tinubu ya taya Abba Kabir murnar cika shekaru 63 da haihuwa, yana yabon halayyarsa da jajircewarsa a mulki
  • Shugaba ya ce salon mulkin Yusuf na mayar da hankali kan talakawa da ci gaban kasa wanda ya yi daidai da akidar Malam Aminu Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Tinubu ya tura sakon taya murnar yayin da gwamnan zai cika shekaru 63 a duniya a ranar 5 ga Janairu, 2026, yana mai yabon jagorancinsa da kokarinsa wajen hidimar al’umma.

Tinubu ya taya Abba Kabir murnar cika shekaru 63
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf. Hoto: Bayo Onanuga, Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya wallafa a X a yau Lahadi 4 ga watan Disambar 2026.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Wike ya hango abin da zai zama karshensa a siyasa

Ayyukan Abba Kabir a Kano sun burge Tinubu

Tinubu ya bayyana Gwamna Yusuf a matsayin shugaba mai mutunci, kan-kan da kai, saukin kai da jajircewa wajen aikin gwamnati, yana mai cewa wadannan halaye sun bayyana karara a yadda yake tafiyar da harkokin Jihar Kano.

Gwamna Abba Yusuf ya hau mulki ne a shekarar 2023 karkashin jam’iyyar NNPP, Kafin haka, ya taba rike mukamin Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri a Kano daga 2011 zuwa 2015, a zamanin tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Shugaba Tinubu ya ce salon mulkin Gwamna Abba Kabir a Kano wadda ya bayyana a matsayin tushen siyasar cigaba a Arewa na nuna jajircewa wajen bunkasa ci gaban kasa daga tushe tare da rage radadin talauci, kamar yadda marigayi Malam Aminu Kano ya assasa tun da dadewa.

A cewarsa:

“Kwarewar jagorancin Gwamna Yusuf, musamman shekarunsa a matsayin kwamishina inda ya kula da muhimman ma’aikatu a Kano, sun shirya shi yadda ya kamata ga sauye-sauyen gine-gine da ake gani a jihar a yau.”

Kara karanta wannan

Bayan shirin barin Kwankwaso, da gaske Abba Kabir zai tarbi Aminu Ado Bayero?

Tinubu ya tuna ayyukan alherin Abba Kabir a Kano
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Yadda Tinubu ya yabawa Abba Kabir

Tinubu ya kara da cewa gwamnan ya kaddamar da shirye-shiryen sabunta birane, tare da gina gadoji da hanyoyin mota, ciki har da shimfida tituna masu tsawon kilomita biyar a kowace karamar hukuma a fadin jihar.

Har ila yau, shugaban kasar ya yaba da ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi da Gwamna Yusuf ya yi, yana mai cewa hakan ya haifar da karuwar nasarar daliban Kano a jarabawar NECO.

A karshe, Shugaba Tinubu ya yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf fatan tsawon rai da karin shekaru na jagoranci mai sauyi, domin ci gaba da samar da cigaba a Jihar Kano da al’ummarta.

Abba Kabir ya fadawa Tinubu halin rashin tsaro

Kun ji cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa rahoton halin tsaro da jiharsa ke ciki ya karasa kunnen Shugaban Kasa, Bola Tinubu.

Ya bayyana cewa tuni Shugaban ya bayar da umarnin kawo wa Kano agaji ta hanyar aiko tawagar tsaro ta musamman zuwa sassan jihar.

Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa yana aiki tukuru domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a, tare da daukan matakai na musamman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.