Harin 'Yan Bindiga: Sojoji Sun Yi Ruwan Bama Bamai a Kano, An Kashe Miyagu 23

Harin 'Yan Bindiga: Sojoji Sun Yi Ruwan Bama Bamai a Kano, An Kashe Miyagu 23

  • Sojojin Najeriya sun hallaka yan bindiga ashirin da uku ta hanyar harin sama bayan sun tsere daga jihar Kano zuwa jihar Katsina
  • Dakarun hadin gwiwa sun dakile harin da yan ta'addan suka kai Shanono da Tsanyawa inda suka lalata makamai da babura masu yawa
  • Kwamandan rundunar ya yaba wa jajircewar dakarun sojojin tare da tabbatar wa mazauna jihar Kano cewa tsaro ya samu yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Dakarun haɗin gwiwa na rundunar Operation Fansan Yamma, tare da goyon bayan sojojin sama, sun yi nasarar hallaka aƙalla 'yan bindiga 23.

An rahoto cewa waɗanda 'yan ta'addar ne suka tsere daga jihar Kano bayan sun kai hare-hare a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Kano
Jirgin sojojin sama ya saki bama bamai kan maboyar 'yan ta'adda. Hoto: @NigAirForce
Source: Twitter

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Kano

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga a Kano

Mataimakin Daraktan yaɗa labarai na 3 Brigade ta rundunar sojin ƙasa, Manjo Zubairu Babatunde, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Kano ranar Lahadi, in ji rahoton Punch.

Manjo Zubairu Babatunde ya bayyana cewa dakarun sojojin ƙasa sun fara dakile wannan harin ne tun daren ranar Alhamis zuwa safiyar ranar Juma'a.

Bayan dakarun ƙasa sun fatattaki maharan a yankunan Yankwada da Babanduhu na jihar Kano, sai suka bi sawun su har zuwa ƙauyen Karaduwa da ke ƙaramar hukumar Matazu a maƙwabcinsu jihar Katsina.

Rahotannin sirri sun nuna cewa 'yan bindigar sun taru ne a yankin Dan Marke domin binne wasu mambobinsu da sojoji suka kashe a fafatawar farko.

an kwato makamai daga hannun 'yan bindiga

A nan ne dakarun sararin samaniya suka gano inda suke tare da kai musu harin bam na ruguntsumi a daidai lokacin da baburansu suka taru wuri ɗaya.

Manjo Babatunde ya ƙara da cewa wannan harin saman ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan ta'adda 23 nan take, yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi dirar mikiya a kasuwa, an rasa rayukan mutane da dama a Neja

Haka kuma, an lalata makamai da kayayyakin aiki masu yawa waɗanda 'yan bindigar ke amfani da su wajen addabar jama'a, in ji rahoton Vanguard.

Kwamandan Birgediya ta 3 ya jinjina wa ƙoƙarin dakarun sama da na ƙasa bisa jajircewa da kishin ƙasa da suka nuna wajen murƙushe maƙiya.

An ce an kashe 'yan ta'addar ne bayan harin da suka kai garuruwan Kano.
Taswirar jihar Kano, inda 'yan ta'adda suka farmaki garuruwa biyu. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji sun matsawa 'yan ta'adda lamba

A halin yanzu, rundunar sojin ta tabbatar da cewa yanayin rashin tsaro a jihar Kano ya ragu sosai, kuma jami'ai suna ci gaba da gudanar da sintiri na kakkaba.

Rundunar ta kuma gode wa mazauna yankin bisa goyon bayan da suke bayarwa ta hanyar bayar da bayanan sirri akan lokaci.

Wannan nasara na zuwa ne a matsayin martani ga 'yan bindigar da suka yi ƙoƙarin ɗaukar fansa bayan asarar da suka yi a hannun sojoji a makon da ya gabata.

Sojoji sun fafata da 'yan bindiga a Kano

A wani labari, mun ruwaito cewa, dakarun hadin gwiwa na JTF da ke Faruruwa sun kai wani sumame na tsaro da suka kai a kan iyakar Kano–Katsina.

Rundunar sojojin Najeriya ta Brigade 3 Kano ta ce an kai samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri na motsin 'yan bindiga a yankunan Daurawa da ke Kira zuwa Kano.

Abubuwan da aka kwato a wajen sun haɗa da babura uku da ‘yan bindigar suka bari yayin tserewarsu, da kuma adadin shanu da ba a bayyana yawansu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com