Dakarun Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Bindiga a Kano
- Dakarun sojojin Najeriya sun kaddamar da hare-hare kan 'yan bindiga masu dauke da makamai a jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yamma
- Sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun farmaki 'yan bindigan ne bayan sun halarci jana'izar wasu 'yan uwansu da jami'an tsaro suka hallaka
- Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindiga sama da 20 sun bakunci lahira bayan an yi musu ruwan wuta da jiragen yaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma sun hallaka ‘yan bindiga 23 bayan wasu hare-hare na hadin gwiwa da aka kai a jihar Kano.
Sojojin sun kai hare-haren ne tsakanin ranakun 1 zuwa 2 ga watan Janairun 2026, lamarin da ke kara tabbatar da ingancin ayyukan tsaro bisa sahihan bayanan sirri da ake ci gaba da gudanarwa a yankin.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa wata sahihiyar majiya daga bangaren sojoji ta shaida wa manema labarai kai harin.
Sojoji sun fafata da 'yan bindiga
Majiyar ta bayyana cewa dakarun sun fafata da ‘yan bindigan ne a kananan hukumomin Shanono da Tsanyawa.
Sojojin sun kai farmakin ne bayan samun bayanan sirri kan inda 'yan bindigan suke yayin da suka je halartar jana’izar wasu ‘yan uwansu da aka kashe a wata arangama da jami’an tsaro a Dan Marke, karamar hukumar Matazu.
Majiyar ta ce dakarun sun bibiyi ‘yan bindigan da ke kan babura 20, wadanda suka taru a bakin wani kwarin kogi da ya bushe a Kauyen Karaduwa, karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina.
An yi wa 'yan bindiga ruwan wuta
Jirgin jirgin yaki na rundunar sojojin sama ya kai musu hari tare da haddasa asara mai yawa, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.
“Aikin leken asiri da bin diddigi ya bi sawun ‘yan bindigan da ke tafiya a kan babura 50, har zuwa lokacin da babura 20 suka taru a bakin wani kwarin kogi da ya bushe."
“Da misalin karfe 17:11 na ranar Asabar, 3 ga Janairu, wani harin jirgin yaki ya kai hari kan ‘yan bindigan da suka taru a kauyen Karaduwa, karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina, inda aka yi musu mummunan lahani."
- wata majiya

Source: Original
Majiyar ta kara da cewa mutuwar ‘yan bindiga 23 ta tabbata bisa rahotannin mutanen da suka ziyarci wajen, sai dai har yanzu ba a fayyace irin kayan da suka rasa ba.
Ta kuma ce yanayin tsaro a jihar Kano yana cikin kwanciyar hankali, yayin da dakarun ke ci gaba da sa ido sosai kan duk wani sabon motsi ko barazana a yankin.
'Yan bindiga sun kai hari a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.
'Yan bindigan sun hallaka mutane akalla 30 tar da sace wasu da dama bayan sun yi dirar mikiya a wata kasuwa.
Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce ta fara yunkurin ceto mutanen da aka sace.
Asali: Legit.ng

