'Yan Bindiga Sun Yi Dirar Mikiya a Kasuwa, an Rasa Rayukan Mutane da Dama a Neja
- An shiga jimami a jihar Neja bayan wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka kai wani harin ta'addanci a wata kasuwa
- Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka mutane da dama tare da yin garkuwa da ba a san adadinsu ba zuwa cikin daji
- Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta tabbatar da aukuwar lamarin tare da bayyana irin kokarin da take yi domin ceto wadanda aka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Akalla mutane 30, ciki har da mata, sun rasa rayukansu a ranar Asabar, 3 ga watan Janairun 2026 sakamakon wani harin ‘yan bindiga.
'Yan bindigan sun kai harin ne a Kasuwar Daji da ke cikin yankin Demo a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta gano cewa maharan sun mamaye yankin ne da misalin karfe 4:00 na yammacin Asabar, inda suka ci gaba da ta’addanci har zuwa safiyar Lahadi, 4 ga watan Janairun 2026.
'Yan bindiga sun yi barna a Neja
‘Yan bindigan sun kuma kwashe kayan abinci da wasu kayayyaki masu darajar miliyoyin naira, kafin daga bisani su cinna wa kasuwar wuta, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da hakan.
Rahotanni sun kuma nuna cewa adadin mutanen da aka sace bai fito fili ba yayin harin.
Wani mazaunin yankin, ya ce fiye da mutane 50 aka daure aka kashe ba tare da wata turjiya ba, yana mai cewa ‘yan bindigan sun yi ta’adi cikin sauki.
An ce maharan sun fito ne daga gandun dajin da ke cikin karamar hukumar Borgu, inda suka kai harin da tsakar yammaci.
'Yan sanda sun yi bayani kan harin
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce sama da mutane 30 ne suka mutu, yayin da aka sace wasu da dama.
“A ranar 03/01/2026 da misalin karfe 9:00 na dare, an samu bayanai cewa da misalin 4:30 na yammacin ranar, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne daga dajin National Park a yankin karamar hukumar Borgu ta hanyar Gundumar Kabe, sun kai hari Kasuwan Daji da ke kauyen Demo."

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarki mai martaba, sun nemi fansar Naira miliyan 450
"Inda suka kona kasuwar, suka wawashe shaguna tare da kwashe kayan abinci."
“A ranar 04/01/2026 da misalin 8:00 na safe, rahoto ya nuna cewa tawagar jami’an tsaro na hadin gwiwa sun kai ziyara wurin, inda aka tabbatar da cewa sama da mutane 30 sun rasa rayukansu a harin."
"An kuma sace wasu mutane. Ana ci gaba da kokarin ceto wadanda aka sace, kuma za a sanar da jama’a duk wani sabon bayani nan gaba.”
- SP Wasiu Abiodun

Source: Original
Rashin imanin ya yi yawa
Wani mazaunin jihar Neja mai suna Kabir Abubakar ya nuna takaicinsa kan mummunan harin da 'yan bindigan suka kai yayin zantawarsa da Legit Hausa.
Ya bayyana cewa akwai rashin imani a daure mutum mai daraja sannan a bude masa wuta ba tare da aikata laifin komai ba.
"Wannan abu sai dai mu ce Allah ya kawo mana karshensa kawai. Amma wannan rashin imanin ya yi yawa sosai."
"Mutanen nan kullum suna ci gaba da hana bayin Allah gudanar da harkokinsu na rayuwa. Muna rokon Allah ya yi mana maganinsu."
- Kabir Abubakar
'Yan bindiga sun kashe mutane a Kebbi
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.
'Yan bindigan sun hallaka mutane takwas a hare-haren da suka kai a wasu kauyuka na karamar hukumar ta Shanga.
Daruruwan mazauna yankin sun tsere daga gidajensu domin neman tsira a garin Shanga da sauran yankunan da ake ganin akwai tsaro.
Asali: Legit.ng

