Duk da Maganganu, An Fadi Nasarar da Aka Samu bayan Harin Amurka a Sokoto

Duk da Maganganu, An Fadi Nasarar da Aka Samu bayan Harin Amurka a Sokoto

  • Rahotanni sun nuna harin sama da Amurka ta kai a daren Kirsimeti ya lalata sansanonin Lakurawa a dazukan Sokoto
  • Mazauna Tangaza sun ce sun ga makamai masu linzami suna afkawa sansanonin Kawuri-Kandam, Malgam da Kahuri
  • Jami’an tsaro sun tabbatar da nasarar harin, suna cewa fiye da makamai 16 aka harba, kuma yanzu babu wata alamar Lakurawa a yankunan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Sababbin bincike sun nuna cewa hare-haren sama da Amurka ta kai a daren Kirsimeti sun lalata sansanonin ’yan ta’addan Lakurawa a Sokoto.

An ce harin ya tilasta wasu daga cikin mayakan Lakurawa tserewa wanda har yanzu babu duriyarsu a yankunan.

An ga amfanin harin da Amurka ta kai jihar Sokoto
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump na Amurka. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Mazauna Sokoto sun magantu kan harin Amurka

Mazauna kauyukan Kawuri-Kandam, Malgam da Kahuri a karamar hukumar Tangaza sun shaida wa Punch cewa sun ga makamai masu linzami suna afkawa sansanonin ’yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kutsa dajin Sambisa, sun yi kaca kaca da Boko Haram

Sun bayyana harin a matsayin abin firgici, inda aka ga wuta da girgizar kasa yayin da makamai ke sauka kan sansanonin Lakurawa.

Sai dai an samu ce-ce-ku-ce kan nasarar harin, inda wasu suka yi ikirarin cewa makamai sun fado a wuraren da ba sansanonin ’yan ta’adda ba.

Jami'in tsaro ya magantu kan harin Amurka

Wani babban jami’in tsaro ya shaida cewa harin ya yi nasara sosai, inda aka harba fiye da makamai 16 kan sansanonin Lakurawa.

Ya ce saboda kasancewar sansanonin a cikin daji mai zurfi, ya yi wahala a samu hotuna ko bidiyon shaidar harin.

Wani jami’in tsaro a Tangaza ya ce harin ya girgiza ayyukan Lakurawa, tare da lalata sansanoni da dama.

Mazauna Tangaza sun ce tun bayan harin, babu wata alamar ’yan ta’adda a yankunan Kawuri-Kandam, Malgam da Kahuri.

Wani mazaunin Tangaza, Abubakar Shehu, ya ce zaman lafiya ya fara dawowa bayan hare-haren.

Ya ce girgizar kasa da wuta sun tsoratar da ’yan ta’addan, inda aka ga suna tserewa da babura zuwa gabas.

Yadda harin Amurka ya tarwatsa Yan ta'adda
Taswirar jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda harin Amurka ya rikita al'umma

Kara karanta wannan

Gyare gyare da alkawuran da majalisar wakilai ta gaza cikawa a 2025

Wani mazauni, Mallam Umar Aliyu, ya ce sun ji karar fashewar abubuwa sau uku, kuma daga baya suka ga wuta a sansanonin.

Ya ce a halin yanzu babu wata alamar Lakurawa a Kahuri, Kandam ko Malgam, domin duk sun gudu.

Wani dillalin maganin gargajiya, Nafiu Umar, ya ce ’yan Lakurawa sun lalata masa hanyar samun abin rayuwa.

Ya ce yanzu yana rayuwa cikin tsoro, yana gujewa fitowa fili duk da kwanciyar hankali da ya fara dawowa.

Bello Abdullah, tsohon dan kasuwa, ya ce an fatattaki al’ummarsa gaba daya kafin sojoji su kara sintiri.

Ya bukaci ci gaba da goyon bayan sojojin Najeriya, yana mai cewa hakan ne kadai zai tabbatar da dorewar zaman lafiya.

Sheikh Gumi ya caccaki harin Amurka a Sokoto

Kun ji cewa Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Dr. Ahmad Gumi ya magantu game da harin Amurka a wasu jihohin kasar guda biyu.

Gumi ya ce Najeriya na bukatar taimakon kasashen waje kan tsaro, amma ba daga masu laifuffuka, wariya ko masu tayar da zaune tsaye ba.

Malamin ya fadi haka ne a kafar sadarwa inda ya nuna damuwa kan irin kasashen ko kungiyoyin da ake neman taimakon tsaro daga gare su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.