Yunkurin Kifar da Gwamnatin Tinubu: An Cafke Babban Malamin Musulunci a Zaria
- Jami'an tsaro sun cafke tare da ci gaba da tsare Sheikh Sani Khalifa Zaria tsawon kwanaki 23 kan zargin alaka da shirin juyin mulki
- Iyalan malamin sun bayyana cewa kudin da aka tura masa kyauta ce ta neman addu'a daga wani soja, ba wai kudin cin amanar kasa ba
- Masu fafutuka na kiran gwamnati da ta saki malamin tunda bincike ya nuna ba shi da masaniya kan wani shirin hambarar da Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke birnin Zaria, Sheikh Sani Khalifa, ya shafe kwanaki 23 a tsare a hannun jami’an tsaro.
Ana zargin Sheikh Sani Khalifa da hannu a wani shirin juyin mulki da aka shira don a kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Twitter
Yunkurin juyin mulki da kama malami
Rahoton Premium Times ya nuna cewa an kama malamin ne a birnin Abuja, jim kaɗan bayan ya tafi can domin warware matsalar rufe asusunsa na banki da aka yi ba tare da wani bayani ba.
Wannan tsarewa na zuwa ne duk da cewa gwamnatin Najeriya ta fito fili ta musanta jita-jitar wani shirin juyin mulki a ƙasar.
Sai dai bincike ya nuna cewa an kama wasu manyan sojoji da ake zargi da shirin hambarar da gwamnatin a ranar 27 ga watan Oktoba.
An bayyana cewa dalilin da ya sa ake tsare da Sheikh Khalifa shi ne an tura masa Naira miliyan biyu daga asusunsa ɗaya daga cikin sojojin da ake zargi.
Iyalai sun fadi dalilin tura wa malami kudi
Iyalai da almajiran malamin sun bayyana cewa Sheikh Khalifa ba shi da wata alaƙa ta kai-tsaye da sojan da ake zargin.
Sun bayyana cewa tura kuɗin ya faru ne ta hannun ɗaya daga cikin almajiran malamin wanda ya san sojan.
Sojan ya nemi lambar asusun malamin ne domin ba shi kyautar kuɗi don neman addu’o'i da albarka, kamar yadda mutane da dama ke yi wa malamai, ba tare da wata tattaunawa ta siyasa ko cin amanar ƙasa ba a cewar iyalan.

Source: Twitter
Ci gaba tsare malamin Musulunci
Duk da cewa majiyoyi sun nuna cewa jami’an tsaro sun kammala bincike kuma sun wanke malamin daga zargin, har yanzu an ƙi sakin sa ko kai shi gaban kotu.
Jaridar ta ce wannan ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya da dokokin haƙƙin ɗan adam na duniya, waɗanda suka haramta tsare mutum na tsawon lokaci ba tare da tuhuma ba.
Iyalansa da almajiransa na ci gaba da yin kira ga gwamnati da ta gaggauta sakin Sheikh Sani Khalifa Zaria tunda ba a same shi da wani laifi ba.
An cafke mai kiran a kifar da Tinubu
A wani labari, mun ruwaito cewa, jami'an hukumar tsaro ta DSS ta kama wani matashi da ake zargi da kiran juyin mulki a kafar sada zumunta.
An gano wanda ake zargi a Oyigbo, jihar Ribas, bayan ya wallafa sakonnin tada zaune-tsaye kan shafinsa na sada zumunta.
Rahotanni sun ce jami'an DSS na ci gaba da bincike kuma wanda ake zargin yana ba da hadin kai yayin da aka rufe shafinsa.
Asali: Legit.ng


