Bayan Shirin Barin Kwankwaso, da Gaske Abba Kabir zai Tarbi Aminu Ado Bayero?
- Gwamnatin Jihar Kano ta yi bayani kan rade radin cewa tana da hannu a sanarwar da ke yawo kan Abba Kabir Yusuf zai jagoranci tarbar Aminu Ado Bayero
- Mai magana da yawun gwamnan ne ya yi karin bayani ga jama'ar Kano yayin da labarin ya karade kafafen sada zumunta a yau, Asabar 3 ga Janairun 2026
- Lamarin ya sake tayar da kura game da rikicin da aka dauki lokaci ana yi a masarautar Kano tsakanin bangarorin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana karara cewa ba ta da wata alaka da sanarwar da ke yawo a kafafen sada zumunta wadda ke ikirarin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai tarbi, Aminu Ado Bayero, yayin dawowarsa jihar.
Wannan bayani ya zo ne bayan fitar wata sanarwa da ke gayyatar al’ummar Kano zuwa filin jirgin saman Malam Aminu Kano domin tarbar Aminu Ado Bayero.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai game da labarin ne a wani sako da mai magana da yawun Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a Facebook.
Sanarwar ta janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, musamman a daidai lokacin da ake ci gaba da rade-radin sauya sheka a siyasar Kano da kuma rikicin masarautar da bai kai ga karshe ba.
Gwamna Abba ba zai tarbi Aminu Ado ba
Sanusi Bature Dawakin Tofa ya musanta zargin cewa gwamnan zai jagoranci shirin tarbar mai martaba Aminu Ado Bayero a Kano.
A cewarsa, babu ruwan gwamna da batun tarbar Aminu Ado Bayero gobe, Lahadi, 4 ga Janairun 2026, yana mai tabbatar da cewa kirkirarren labari ne.
Maganar ta nuna cewa gwamnatin jihar ba ta fitar da wata sanarwa ko umarni dangane da tarbar Aminu Ado Bayero da ake yadawa ba.
Labarin da aka fitar kan Aminu Ado
Sanarwar da ke yawo, wadda aka ce ta fito daga wani “Kwamitin Shirye-shirye”, ta bayyana cewa za a tarbi tawagar Alhaji Aminu Ado Bayero, a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano bayan dawowarsa gida.
Sanarwar ta kuma bukaci masoyansa da daukacin al’ummar Kano da su fito cikin natsuwa da tsari, tare da addu’ar samun lafiya da tsawon rai ga mai martaban.
Sai dai gwamnatin jihar Kano ta ce wannan sanarwa ba ta da alaka da ita, kuma ba ta wakiltar matsayar hukuma ko ta fadar gwamnati.

Source: Facebook
Asalin rikicin masarautar Kano
Aminu Ado Bayero dai na cikin rikicin masarautar Kano tun bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tube shi daga sarautar Sarkin Kano tare da mayar da Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki.
Tun daga wannan lokaci, rikicin ya koma kotuna, inda ake ci gaba da shari’o’i kan halaccin sarautar Kano, lamarin da ya sa ake da mutane biyu da ke ikirarin kasancewa halattattun sarakuna.
Ganduje zai karbi Abba Kabir a APC
A wani labarin, kun ji cewa wani rahoto ya nuna cewa manyan jam'iyyar APC za su karbi gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.
A bayanan da Legit Hausa ta samu, an ce mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima na cikin wadanda za su karbi gwamnan.
Baya ga Shettima, An bayyana cewa Abdullahi Umar Ganduje da shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas na cikin wadanda za su karbi Abba Kabir.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

