Asiri Ya Tonu: Sojoji Sun Cafke Jagoran 'Yan Kunar Bakin Waken Masallaci a Borno
- Dakarun sojojin Najeriya na ci gaba da samun nasara a yakin da suke yi kan ayyukan ta'addanci a yankin Arewa maso Gabas
- Sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasarar cafke jagoran wata kungiyar 'yan kunar bakin wake a jihar Borno
- Wanda aka cafken na da hannu kan hari bam a masallacin Maiduguri da yunkurin kai hare-hare a yankin Arewa maso Gabas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Sojojin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun gano tare da cafke Shariff Umar, wanda aka fi sani da Yusuf, a matsayin babban mai tsarawa da jagorantar hare-haren kunar bakin wake a Borno.
Jagoran dai na da hannu kan kai hare-hare da yunkurin kai hare-hare da aka kai kwanan nan a yankin Arewa maso Gabas.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Sojoji sun cafke jagoran 'yan kunar bakin wake
Ya ce rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cafke wanda ake zargin bayan wani samamen bincike na sirri da aka gudanar a yankin Kalmari da ke Maiduguri a ranar 31 ga Disamba, 2025.
Aikin kai samamen ya kai ga cafke mutane 14 da ake zargi suna da hannu a ayyukan kunar bakin wake, inda bincike daga baya ya fallasa tsarin tawagar, rawar da kowa ke takawa da hanyoyin sadarwarta.
An ce wani da ake zargin mai shirin kai harin kunar bakin wake, Ibrahim Muhammad, wanda ke tsare a hannun jami’an tsaro, ya bayyana Shariff Umar a matsayin shugaban kungiyar, wanda ke daukar ma’aikata, shirya su tare da aikawa da su wuraren da ake son kai hari.
“Maganganu masu tabbatar da juna sun nuna cewa Shariff Umar ne ke daidaita harkokin sufuri da samar da sassan bam (IED) da ake amfani da su wajen hare-haren kunar bakin wake."
- Rundunar sojoji
Ya shirya kai harin bam a masallaci
Sojojin sun kara da cewa bincike ya tabbatar da cewa Shariff Umar ne kai tsaye ya shirya harin kunar bakin wake da aka kai a Masallacin Kasuwar Gamboru a ranar 24 ga Disamba, 2025, inda wani abokinsa mai suna Adamu ya tayar da bam din jikinsa tare da rasa ransa.
Haka kuma, an danganta Shariff Umar da yunkurin harin kunar bakin wake da aka dakile a Damaturu, inda aka ce shi da kansa ne ya mika sassan bam din ga wanda zai kai harin a Maiduguri.
Sanarwar ta ce bayanan sirri sun kuma nuna rawar da matar Shariff Umar, Yagana Modu, ta taka, yayin da ’yar da yake riko, Amina, ta tabbatar da cewa ta ga wanda ake zargin ya kai harin a cikin gidansu kafin faruwar lamarin.
“Wadannan bayanai sun fallasa yadda ‘yan ta’adda ke amfani da boye-boye a cikin gida da al’umma domin gudanar da ayyukansu."
- Rundunar sojoji

Source: Original
Mutanen da sojoji su ka cafke na tsare
Rundunar sojojin ta ce duk wadanda aka cafke har yanzu suna tsare, kuma ana ci gaba da zurfafa bincike domin tarwatsa ragowar tawagar da kwato duk wani bam ko kayan aiki da suka rage.
Sojojin sun jaddada cewa wannan nasara ta nuna muhimmancin hadin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma, inda suka ce yawancin kungiyoyin ‘yan ta’adda na rayuwa ne ta hanyar boyewa cikin jama’a.
Sun kuma bukaci al’umma da su kasance masu sa ido, tare da gaggauta sanar da jami’an tsaro duk wani mutum ko abu da ake zargi, suna mai cewa ci gaba da hadin kai shi ne mabuɗin hana hare-hare da dawo da zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Sojoji sun ragargaji 'yan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram.
Dakarun sojojin na rundunar Operation Hadin Kai wadamda suka kai samamen a dajin Sambisa, sun hallaka ’yan Boko Haram tare da kwato makamai.
Majiyoyi sun bayyana cewa dakarun Najeriya ne suka jagoranci samamen, tare da hadin gwiwar CJTF, rundunonin hadaka da kuma mafarauta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


