Tsohon Dan Majalisa da Aka Sace a Masallaci Ya Samu ’Yanci bayan Biyan N50m

Tsohon Dan Majalisa da Aka Sace a Masallaci Ya Samu ’Yanci bayan Biyan N50m

  • Tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Ogun, Hon. Musa Moruf, ya samu ’yanci bayan kwana uku a hannun masu garkuwa da mutane
  • Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun saki tsohon ɗan majalisar ne bayan an biya kudin fansa har Naira miliyan 50
  • Mazauna Ogun Waterside sun nemi a ƙara tsaro, suna cewa yankin na buƙatar kulawa ta musamman domin kare rayuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Ogun, Hon. Musa Moruf, ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane.

'Dan siyasar ya samu 'yanci ne bayan shafe kwana uku a tsare inda aka tabbatar da cewa sai da aka biya kudin fansa.

Tsohon dan majalisa ya kubuta daga hannun yan bindiga
Kakakin yan sanda a Ogun, DSP Oluseyi Babaseyi. Hoto: Ogun State Police Command .
Source: Facebook

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Tribune cewa tsohon ɗan majalisar ya samu ’yanci ne a daren Juma’a 2 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Jirgin saman sojoji ya yi hatsari a kokarin yaki da 'yan ta'adda a Niger

Yadda 'yan bindiga suka sace Moruf a masallaci

An tabbatar da cewa hakan ya faru ne bayan da masu garkuwar suka karɓi kudin fansa har Naira miliyan 50 daga iyalansa.

An dai sace Musa Moruf, wanda ya taɓa zama ɗan majalisar dokoki a majalisa ta shida ta Jihar Ogun ne da misalin ƙarfe 7:00 na yamma, yayin da yake sallar magariba a wani masallaci da ke Ibiade, a Ƙaramar Hukumar Ogun Waterside.

Rahotanni sun nuna cewa masu garkuwar sun yi awon gaba da shi zuwa cikin wani daji mai duhu bayan dauke shi a masallacin, cewar Punch.

Tsohon dan majalisa ya shaki iskar 'yanci daga 'yan bindiga
Taswirar jihar Ogun da ke fama da masu garkuwa da mutane. Hoto: Legit.
Source: Original

Miliyoyin da aka biya 'yan bindiga a Ogun

Majiyoyi sun tabbatar da cewa 'yan bindigar sun saki dan siyasar ne bayan biyan makudan kudi na fansa har N50m.

Majiyar ta ce:

“An saki Hon. Musa Moruf. Masu garkuwar sun tuntube mu tare da neman Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa. An tara kuɗin kuma an kai musu, daga nan ne suka sake shi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarki mai martaba, sun nemi fansar Naira miliyan 450

“Masu garkuwar Fulani ne, kuma suna da hanyar sadarwa ta daban, Yanzu haka ɗan’uwanmu ya koma gida lafiya kalau.”

Majiyar ta ƙara da cewa akwai buƙatar a ƙarfafa tsaro a Ƙaramar Hukumar Ogun Waterside, inda ta ce yanayin yankin na buƙatar kulawa ta musamman domin kare rayukan al’umma.

Ta kuma bayyana cewa an kai kudin fansar ne zuwa hannun masu laifin a ɗaya daga cikin jihohin Arewa ta Tsakiya, tare da kira da a tura ƙarin jami’an tsaro domin tabbatar da tsaron yankin.

Kakakin yan sanda ya tattauna da Legit Hausa

Kakakin rundunar yan sanda a Ogun, Oluseyi Babaseyi ya tabbatar da nasarar da aka samu bayan dan siyasar ya shaki iskar yanci ga wakilin Legit Hausa.

Babaseyi ya ce jami'an tsaro na ci gaba da sintiri a yankin domin tabbatar da tsaro da hana afkuwar sace-sace.

Ya ce:

"An sake shi, kuma jami’anmu na ci gaba da aiki tukuru a yankin Waterside domin tabbatar da cewa yankin na cikin cikakkiyar tsaro."

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ogun, Oluseyi Babaseyi, bai fitar da wata sanarwa ba dangane da sakin tsohon ɗan majalisar.

Kara karanta wannan

Abun ya yi muni: 'Yan bindiga sun kai mummunan hari Kebbi, an rasa rayuka

'Yan bindiga sun kashe tsohon dan majalisa

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Imo ta yi alkawarin yin duk abin da ya dace don ganin ta ceto Ngozi Ogbu, tsohon ɗan majisa da aka sace.

A ranar 7 ga Satumba, 2025 ne wasu da ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne, ɗauke da makamai suka sace Mista Ngozi.

Wadanda suka sace tsohon dan majalisar, sun ce za su kashe shi idan gwamnati ba ta biya bukatunsu a kwanaki hudu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.