Gwamna Bago Ya Bude Makarantu bayan Ceto Dalibai Fiye da 200 daga Hannun 'Yan Bindiga

Gwamna Bago Ya Bude Makarantu bayan Ceto Dalibai Fiye da 200 daga Hannun 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin jihar Neja ta sanar da bude duka makarantun gwamnati da na kudi da aka rufe sakamakon tabarbarewar tsaro a kwanakin baya
  • Kwamishinar kula da harkokin ilimin firamare da sakandire ta Neja, Dr. Hadiza Asebe Mohammed ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar
  • Ta ce hakan ya biyo bayan ceto duk daliban makarantar Papiri da 'yan bindiga suka sace, da kuma shawarwarin hukumomin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Gwamna Mohammed Umaru Bago ya amince da sake bude makarantun gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar Neja.

Wannan mataki ya biyo bayan rufe makarantun da aka yi kwanakin baya sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai tare da sace dalibai da malamai a makarantar Papiri.

Gwamna Mohammed Umaru Bago.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago a gidan gwamnati a Minna Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Dalilan dakatar da karatu a makarantun Neja

Leadership ta ruwaito cewa gwamnan jihar Neja ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantu ne bayan sace kimanin dalibai da ma’aikata 230 na makarantar St. Mary Catholic, Papiri a ranar 21 ga Nuwamba, 2025,

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kashe bayin Allah ana tsaka da murnar shiga 2026 a garin Jos

Wannan lamari dai ya dakatar da harkokin karatu, inda manyan makarantun gaba sakandire da ke jihar Neja suka umarci dalibai su koma gida har sai komai ya daidaita.

A yanzu gwamnatin Neja ta sanar da bude makarantun ta hannun kwammishinar ilimi firamare da sakandire ta jihar Neja, Dr. Hadiza Asebe Mohammed.

An bude makarantun gwamnati a jihar Neja

A sanarwar da ta rattaba wa hannu, Dr. Hadiza ta ce za a bude makarantun ne daga ranar 12 ga watan Janauru, 2026.

Ta bayyana cewa duk mutanen da aka sace daga makarantar Katolika da ke garin Papiri a karamar hukumar Agwara sun shaki iskar yanci.

A cewar kwamishinar, jami'an tsaro ne suka samu nasarar ceto daliban daga hannun masu garkuwa da mutane bayan shafe makonni suna tsare, a cikin watan Disamba 2025.

Sanarwar ta ce:

“An dauki matakin bude makarantu ne bayan tantance yanayin tsaro da kuma shawarar da aka yi da hukumomin tsaro.
"Gwamma Mohammed Bago na nan a kan kudurinsa na tabbatar da kare rayuka tare da tabbatar da cewa yara a Jihar Neja suna samun ilimi mai inganci ba tare da tsaiko ba.”

Kara karanta wannan

Kungiyar NLC ta fara gwagwarayar neman karin albashi ana shiga 2026

Jihar Neja.
Taswirar jihar Neja da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamnatin Neja ta kebe wasu makarantu

Sai dai Dr. Hadiza Mohammed ta ce ba za a bude makarantun da ke yankunan da ake ganin ba su da cikakken tsaro ba a halin yanzu ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ta kara da cewa, a wannan lokaci, hukumomin tsaro na tantance dukkan makarantu domin tabbatar da tsaronsu kafin ranar da aka tsara domin sake buɗewa.

Yadda aka ceto daliban Papiri

A wani rahoton, kun ji cewa an kara samun bayanai kan yadda aka ceto daliban makarantar Papiri a jihar Neja da yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Duk da ikirarin gwamnati cewa an saki kowa, har yanzu akwai sabanin alkaluma kan ko an ceto dukkannin daliban da malaman da aka sace tun a farko.

Bisa adadin da Kungiyar kiristoci (CAN) ta fitar, har yanzu akwai ragowar dalibai a hannun masu garkuwa da mutanen.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262