An Yi Wa Netanyahu Taron Dangi kan Yunkurin Kawo Dauki ga Kiristoci a Najeriya
- Firaministan Israila, Benjamin Netanyahu, ya yi magana kan goyon Donald Trump wajen yakar matsalar ta'addanci a Najeriya
- Kalaman Benjamin Netanyahu sun jawo martani mai kaushi daga wasu al'ummar Musulmi a Najeriya wadanda suka ragargaje shi
- Sun bayyana cewa bai kamata mutumin da ke yin kisan kiyashi a Gaza ya rika tsoma baki kan batun yaki da ta'addanci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wasu shugabannin Musulmi a Najeriya sun bukaci Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da ya nisanci harkokin Najeriya.
Hakan na zuwa ne biyo bayan kalamansa na baya-bayan nan inda ya yi alkawarin hada kai da Shugaban Amurka, Donald Trump, wajen yaki da hare-haren ‘yan ta’adda kan Kiristoci a Najeriya.

Source: Facebook
Kungiyar Muslim Ummah of South West Nigeria (MUSWEN) ta yi magana da jaridar Tribune a ranar Juma’a, 2 ga watan Janairun 2026 kan lamarin.

Kara karanta wannan
Israila ta shiga batun muzgunawa Kiristoci a Najeriya, Netanyahu ya fadi shirin da yake yi
Musulmai sun soki Benjamin Netanyahu
Ta bayyana cewa abin mamaki ne yadda Netanyahu, wanda ta zarge shi da laifin ta’addanci kan Falasdinawa, shi ne yake ikirarin son yaki da ta’addanci a Najeriya.
Babban sakataren MUSWEN, Farfesa Wole Abbas, ya ce:
“Maganar Netanyahu cewa zai hada kai da Shugaban Amurka Donald Trump wajen yaki da ta’addanci a Najeriya abin takaici ne."
"Abin da ya aikata wa Falasdinawa a Gaza ya kusan fin ta’addanci muni. Wannan mutum ne da kotun ICC ke nema ruwa a jallo."
"Duk da haka yana ci gaba da aikata kisan kiyashi a Gaza, sannan yana cewa zai taimaka wajen magance matsala makamancin haka a Najeriya. Gaskiya ban fahimci irin wannan duniya da muke ciki ba."
"Netanyahu mutum ne mai laifi da ya kamata a kama shi a gurfanar da shi kan kisan kiyashi.”
Akwai zarge-zarge kan Netanyahu
Haka zalika, tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya yi watsi da ikirarin Netanyahu na cewa Isra’ila za ta hada kai da Amurka wajen kare Kiristocin da ake zalunta a Najeriya.

Kara karanta wannan
Rundunar sojoji ta fara fitar da bayanai kan harin da Amurka ta kai jihar Sakkwato
Bashir Ahmad ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a, 2 ga watan Janairun 2026.
“Najeriya ba ta bukatar taimakonku. Muna maraba da sahihin goyon baya wajen magance matsalolin tsaro, amma ba daga mutanen da ke fuskantar shari’ar kisan kiyashi a gaban kotun kasa da kasa ba.”
- Bashir Ahmad
Me cece manufar Netanyahu kan Najeriya?
A bangare guda, wani jigo a jam’iyyar PDP a jihar Sokoto, Alhaji Kabiru Aliyu, ya yi Allah-wadai da kalaman Firaministan Isra’ila na cewa zai kare Kiristoci a Najeriya.
“Ina da tabbacin ba da gaske yake ba. Da farko, a ina ne ake tsananta wa Kiristoci a Najeriya? Kuma yaushe ne ya zama Kirista da zai kare muradunsu?"
"A bayyane yake cewa shi Bayahude ne, kuma bambancin Bayahude da Kirista ya fi na Kirista da Musulmi nisa."
"Bai kamata ya dauki shiru da haƙurin Najeriya a matsayin rauni ba. Ƙasar na da matsalolin tsaro; ya bar ta ta mai da hankali kan su.”
- Alhaji Kabiru Aliyu

Source: Twitter
Haka kuma, wani jagoran Musulmi a Sokoto, Malam Umar Abubakar, ya ce Firaministan Isra’ila ba wani abu yake nema ba face albarkatun kasa (ma’adinai) na Najeriya.
Fasto ya karyata ikirarin kisan Kiristoci a Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban Darikar Katolika na Sokoto, Bishop Matthew Kukah, ya yi magana kan zargin muzgunawa Kiristoci a Najeriya.
Bishop Matthew Kukah ya fito ya karyata ikirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.
Ya bayyana cewa duk wata magana da ake yi a kasashen waje cewa Kiristoci na fuskantar matsananciyar barazana a Najeriya ba ta da tushe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
