Malaman Musulunci 20,000 daga Amurka, Saudi da Kasashe Sun Hallara Najeriya
- Dubban malaman Musulunci daga kasashe daban-daban sun taru a Lagos domin tattauna batutuwan zaman lafiya da tarbiyya a duniya
- Taron na duniya karo na 17 na Daaru Na’im Academy ya jawo manyan malamai, shugabanni da masana daga Afirka, Asiya, Turai da Amurka
- Tattaunawa na mayar da hankali kan kalubalen zamani da ke fuskantar al’ummomin Musulmi da hanyoyin magance su bisa ilimi da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos – Dubban malaman Musulunci daga Saudiyya, Amurka, Malaysia da wasu kasashe sun hallara a Najeriya domin halartar wani gagarumin taron kasa da kasa da ke da nufin karfafa akida sahihiya a matsayin ginshikin zaman lafiya.
Taron, wanda shi ne karo na 17 na taron duniya na Daaru Na’im Academy, yana gudana ne a Lagos daga 1 zuwa 4, Janairu, 2026.

Kara karanta wannan
Babbar kotun tarayya ta shirya zama kan bukatar da Abubakar Malami ya shigar gabanta

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa taron ya hada malamai, masana ilimi, sarakuna, jami’an gwamnati da shugabannin addini daga sassa daban-daban na duniya.
An bude taron ne a filin sallar Idi na Daaru Na’im da ke kusa da Asibitin Janar na Alimosho a Igando, inda sama da mutane 20,000 suka halarta a zahiri, yayin da dubban wasu suka shiga ta intanet daga kasashe daban-daban.
Dalilin taron Musulmin duniya a Najeriya
Shugaban Daaru Na’im, As-Shaykh Dr Imran AbdulMajeed Eleha, ya bayyana cewa an kira taron ne domin tunkarar kalubalen zamani da ke addabar al’ummomin Musulmi, musamman matsalolin da suka shafi akida, dabi’u da hadin kan jama’a.
Leadership ta rahoto ya ce taron na kwanaki hudu yana mayar da hankali kan sake jaddada muhimmancin akida sahihiya wajen gina nagartattun mutane da al’umma mai dorewar zaman lafiya.
A cewarsa, yawancin matsalolin zamantakewa, dabi’u da rikice-rikicen tunani da ke fuskantar Musulmi a yau na da nasaba da kaucewa akida sahihiya.
Taron ya tara Musulmai daga fadin duniya
Dr Eleha ya jaddada cewa irin wadannan kalubale na bukatar hadin kan malamai bisa ingantattun koyarwar Musulunci tare da amfani da ilimi da hikima wajen magance su.
Taron ya kunshi mahalarta daga Saudiyya, Amurka, Malaysia, Jamhuriyar Benin, Ivory Coast, Aljeriya, Gambia, Togo da sauran kasashe.
Cikin wadanda suka hallara akwai wakilai daga ma’aikatar harkokin addinin Musulunci ta Saudiyya da malamai daga manyan cibiyoyin Musulunci a Amurka da Asiya.
Rahoto ya nuna cewa an gudanar da bikin bude taron da harsuna da dama ciki har da Larabci, Turanci, Faransanci, Hausa da Yarbanci.

Source: Facebook
A madadin Majalisar Koli ta Shari’a a Najeriya, Abubakar Sadiq Muhammad ya bayyana taron a matsayin mai muhimmanci da tasiri, yana mai cewa ya kara jaddada ka’idar tauhidi a matsayin tushen dukkan ibadar Musulunci.
An rantsar da Mamdani da Kur'ani
A wani labarin, mun kawo muku cewa an yi taron rantsar da sabon magajin garin birnin New York na kasar Amurka, Zohran Mamdani.
Mamdani ya sha rantsuwa da Al-Kur'ani mai girma inda ya bayyana cewa zai tabbatar da adalci da cika dukkan alkawuran da ya dauka.
Magajin garin ya kasance Musulmi na farko da ya rike mukamin kuma wanda ya fara shan rantsuwar fara aiki da Al-Kur'ani mai girma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

