Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Sarki Mai Martaba, Sun Nemi Fansar Naira Miliyan 450
- Masu garkuwa da mutane sun fara tattaunawa da iyalan Sarki, dansa da wasu mutane takwas da suka yi garkuwa da su a jihar Kwara
- Rahotanni daga iyalan Sarkin sun nuna cewa 'yan bindigar sun nemi a hada masu Naira miliyan 450 kafin sako wadanda ke hannunsu
- Rundunar yan sanda ta jihar Kwara ta bayyana cewa jami'an tsaro na iya bakin kokarinsu wajen ganin sun kubutar da mutanen cikin koshin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kwara, Nigeria - 'Yan bindigar da suka yi garkuwa da wani Sarki, dansa da wasu mutane takwas sun fara tattaunawa da 'yan uwansu domin karbar kudin fansa a jihar Kwara.
Masu garkuwar sun bukaci Naira miliyan 150 a matsayin kudin fansar basaraken, Oniwo na Aafin, Oba Simeon Olaonipekun, da ɗansa Olaolu, wanda ke yi wa kasa hidima, NYSC.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa yan bindigar sun kuma bukaci a biya Naira miliyan 300 domin sakin mutane takwas da aka sace a Adanla-Irese, wani yanki a Igbaja cikin jihar Kwara.
'Yan bindiga sun tuntubi iyalan Sarki
Wani dan uwa sarkin, wanda ya yi magana da manema labarai a ranar Juma’a ba tare da bayyana sunansa ba, ya tabbatar da cewa masu garkuwar sun tuntube su tun da rana.
“Masu garkuwar sun tuntubi iyalinmu da rana suka ce mu kawo Naira miliyan 150 domin a saki Kabiyesi da ɗansa,” in ji majiyar.
Ya koka da cewa iyalan gidan sarauta sun shiga cikin mummunan yanayi tun bayan sace su, wanda ya faru a daren sabuwar shekara, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.
“Tunda wannan lamari ya faru, ba mu samu natsuwa ba. Mun shiga sabuwar shekara cikin bakin ciki da hawaye. Muna kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su taimaka mana domin ba mu san abin yi ba,” in ji shi.
Masu garkuwa sun nemi jimilla N450m
Kwamandan rundunar yan sa-kai ta Kwara ta Kudu, Elder Olaitan Oyin-Zubair, shi ma ya tabbatar da bukatar kudin fansar da yan bindigan suka aiko.
“Eh, gaskiya ne, ‘yan bindigar sun tuntubi iyalinsa da rana kuma sun bukaci Naira miliyan 150 domin sakin Kabiyesi da ɗansa.
"Kwanaki biyu da suka wuce kuma, an bukaci Naira miliyan 300 domin sakin mutanen Adanla da aka sace,” in ji shi.

Source: Original
Wane mataki hukumomin tsaro suka dauka?
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sanda, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce rundunar ba ta da labarin wata bukatar kudin fansa.
“Ba mu da labarin an nemi kudin fansa domin sakin mutanen da aka sace a Kwara. Kwamishinan ‘Yan Sanda, Adekimi Ojo, ya sha nanata cewa biyan kudin fansa na karfafa ‘yan ta’adda.
“‘Yan sanda da sauran hukumomin tsaro na aiki dare da rana domin ceto wadanda aka sace da kuma kawar da masu aikata laifuffuka daga jihar Kwara,” in ji ta.
'Yan bindiga sun kai hari a jihar Gombe
A wani labarin, kun ji cewa mahara da ba a tantance ko su wanene ba sun kutsa kai cikin wani gida a ƙauyen Pindiga da ke ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe.
An rahoto cewa 'yan bindigan sun kashe wasu 'yan gida daya su biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane huɗu a safiyar ranar Lahadi.
Wannan lamari ya jefa al'ummar yankin cikin babban tsoro da fargaba,.musamman ganin yadda maharan suka yi ta harbi ba kakkautawa a.cikin dare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


