Aure Ya Dauru: An Ji Yadda Sarauniya Zaynab Ta Auri Sakataren Gwamnatin Najeriya
- Amaryar sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ta yi magana bayan daura aurensu da aka yi a asirce kwanakin baya
- Sarauniya Zaynab ta bayyana cewa ta auri Sanata Akume ne saboda kauna, fahimtar juna da kuma manufar da suka yi tarayya a kai
- Ta kuma bayyana cewa wannan aure zai zama alheri ga yan Najeriya saboda ita da angonta duk suna da burin taimakon jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue - Sarauniya Zaynab Ngohemba, amaryar Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, ta bayyana dalilan da suka jawo har aka daura aurensu kwanan nan.
Amarya Zaynab ta bayyana cewa ita da angonta sun samu fahimtar juna, manufa daya, kuma suna da kamala da mutunci, hakan ya sa suka amince su zauna a inuwa daya.

Source: Facebook
An daura auren Akume da Sarauniya Zaynab
Jaridar Leaderahip ta ruwaito cewa Akume ya auri Sarauniya Zaynab, wacce a baya ake kiranta da Zaynab Otiti Obanor, a wani bikin aure na sirri da aka gudanar a 2025.
Auren da aka daura a asirce ya jawo hankalin jama’a musamman a kafafen sada zumunta da kuma fagen siyasa.
An tabbatar da daura auren ne a ranar Juma’a ta hanyar wani sakon taya murna da Abraham Double-D Dajoh, ɗaya daga cikin ‘yan gidan Dajoh, ya fitar.
Sai dai ita ma amarya ta tabbatar da wannan aure a cikin wata sanarwa da mai taimaka mata kan harkokin yaɗa labarai, David Adeoye, ya fitar a ranar Laraba.
Dalilan daura auren Akume da Zaynab
Sarauniya Zaynab ta ce aurenta da Sanata Akume yana nufin haɗuwar mutane biyu da tuni suka sadaukar da rayuwarsu ga hidimar jama’a kuma suka zabi rayuwa tare da juna.
Sanarwar ta ce:
"Soyayya, fahimtar juna da manufa daya ce suka sa aka daura mana aure. Wannan aure na mu ba komai bane face haduwar mutane biyu masu manufar taimakon jama'a.
Amaryar ta kuma bayyana cewa auren ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ƙara neman gaskiya da tausayawa daga masu rike da muƙaman gwamnati.

Source: Facebook
Takaitaccen bayani kan auren Zaynab
Sarauniya Zaynab, wadda a da ake wa lakabi da Olori Wuraola, ta taba auren Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi (Ojaja II), kamar yadda Guardian ta kawo.
An daura aurensu na gargajiya a watan Maris na 2016, amma auren ya mutu a shekarar 2017 bayan kusan watanni 17.
A yanzu kuma, ta auri sakataren gwamnatin tarayya kuma tsohon gwamnan jihar Benuwai, Sanata George Akume.
Uwargidan Akume ya ja hankalinsa
A wani labarin, kun ji cewa ‘yar majalisar tarayya mai wakiltar Gboko/Tarka, Regina Akume, ta ja hankalin mijinta, Sakataren Gwamnatin Tarayya kan riko addinim Kirista.
Regina ta roki George Akume , da kada ya yi watsi da addinin Kiristanci, tana mai jaddada cewa dukkan nasarorin da ya samu a rayuwa sun samo asali ne daga imaninsa.
Regina Akume ta roki Allah da ya ba mijinta tsawon rai, cikakkiyar lafiya da hikima, tare da tunatar da shi muhimmancin tushen imaninsa na Kirista.
Asali: Legit.ng

