Gwamna Bala da Ministan Abuja Sun Ja Daga, Sun Fara Amfani da Kalamai Masu Zafi

Gwamna Bala da Ministan Abuja Sun Ja Daga, Sun Fara Amfani da Kalamai Masu Zafi

  • Rikici tsakanin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike ya dawo danye
  • Gwamna Bala ya zargi Wike ta kokarin cinna wuta a jihar Bauchi kamar yadda ya furta a baya ta hanyar amfani da hukumomin gwamnatin tarayya
  • Wike ya musanta zargin cewa shi ke haddasa rikici a jihar Bauchi, inda ya bukaci Gwamna Bala ya fuskanci matsalolin da ke gabansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Musayar yawu mai zafi ta barke tsakanin Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike.

Wannan cacar baki ta taso ne bayan gurfanar da kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu kan zargin tallafawa ayyukan ta'addanci a Arewacin Najeriya.

Gwamna Bala Mohammed.
Gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban gwamnonin PDP, Bala Mohammed Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

A rahoton Daily Trust, Gwamna Bala ya zargi Wike da wasu jami’an gwamnatin tarayya da kitsa masa shirin muzantawa, tsoratarwa da amfani da hukumomi wajen lalata masa suna.

Kara karanta wannan

Ana rade radin komawa APC, mataimakin gwamnan Kano ya tura sako ga Abba da Kwankwaso

Abin da ya bata wa Gwamna Bala rai

Da yake jawabi a shirin gidan talabijin na Channels TV a ranar Alhamis, Gwamna Bala ya ce Wike na jagorantar wani shiri na zalunci ta hanyar amfani da hukumomin tsaro da na shari’a domin murkushe shi a siyasance.

"Abin da ya fi damu na shi ne ambatar sunana a cikin zargin daukar nauyin ta'addanci domin ban taɓa fuskantar irin waɗannan zarge-zarge ba a rayuwata.
"Ku duba tarihina a matsayin jami’in gwamnati, Sanata da Minista. Akwai mutanen da ke bayan wannan lamarin, kuma na san su,” in ji Bala Mohammed.

Gwamnan Bauchi ya zargi Ministan Abuja

Ya kuma tunatar da cewa Ministan Abuja ya taɓa cewa zai “hura wuta” a jiharsa, yana mai zargin Wike da sarrafa hukumomin gwamnati ba bisa ka'ida ba da ba da cin hanci.

Bala ya ƙara da cewa wasu majiyoyi daga EFCC sun shaida masa cewa ƙorafe-ƙorafe da takardun da ake amfani da su a kotu duk an tsara su ne domin a jefa shi da wasu jami’an gwamnatinsa, ciki har da Kwamishinan Kuɗi, cikin matsala.

Kara karanta wannan

Ana rade radin zai koma APC, Gwamna Abba ya yi jawabi bayan sa hannu kan kasafin 2026

"Ban hana a ambaci sunana ba idan har kwamishina na yana da hannu, amma a jingine kariyar da doka ta ba ni a matsayin gwamna abin takaici ne kuma yana ɓata min suna.”
Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Source: Facebook

Wike ya maida martani ga Gwamna Bala

A nasa martanin, Wike, ya tsokani Gwamna Bala Mohammed, yana mai cewa ba shi da ƙarfi ko tsari a jam’iyyarsa da zai ba shi damar fitar da magaji a jihar Bauchi.

“Bala Mohammed ya zo jihata yana ƙoƙarin kakaba mana shugabanni a PDP. Na faɗa masa ya yi hattara kuma ya bar jihata. Yanzu a jiharsa ma ba zai iya dora magaji ba,” in ji Wike.

Dangane da zargin da Gwamna Bala Mohammed ya yi cewa shi ne ke haddasa rikici a Bauchi, Wike ya musanta hakan gaba ɗaya, yana mai cewa zargin ba shi da tushe.

“Ya ce duk matsalolin da yake fuskanta ni ne sanadi. Ya ce na ce zan hura wuta. Idan yana ganin yana da irin wannan iko, to ya fuskanci matsalolinsa mana,” in ji Wike.

Bala ya yi fatali da zargin alaka da ta'addanci

A baya, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya nuna bacin ransa matukan kan zargin alakanta shi da harkokin ta'addanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Ni ba ɗan ta'adda ba ne': Gwamna Bala ya fusata kan alaƙanta shi da ta'addanci

Gwamnan, wanda ya kusa gama wa'adinsa ya ce ba shi da wata alaƙa da ayyukan ta’addanci ko goyon bayan aikata laifuka a kasar nan.

Ya bayyana fushinsa kan yadda EFCC ke tsare Kwamishinan Kuɗinsa, yana cewa ana amfani da hukumomi wajen muzgunawa ‘yan adawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262