Israila Ta Shiga Batun Muzgunawa Kiristoci a Najeriya, Netanyahu Ya Fadi Shirin da Yake Yi
- Firaministan Israila, Benjamin Netanyahu, ya yi tsokaci kan batun muzgunawa Kiristoci a sassan daban-daban na duniya
- Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa ana muzgunawa Kiristoci a Najeriya kuma a shirye yake ya taimaka musu
- Firaministan na Israila dai ya bayyana kasarsa a matsayin wadda ta fi kowace kasa ba al'ummar Kiristoci kariya a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Amurka - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi magana kan batun muzgunawa Kiristoci a Najeriya.
Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa kasarsa na aiki a kan wani tsari na musamman domin tallafa wa al’ummomin Kiristoci da ke fuskantar matsin lamba a Najeriya.

Source: Twitter
Netanyahu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wani taro da jagororin al’ummar Kiristocin Evangelical a jihar Florida ta Amurka kamar yadda ya sanya a shafinsa na X.
Shugaban Israila na son kare Kiristoci
Firaministan ya bayyana Isra’ila a matsayin kasar da ta fi kowa iya kare Kiristoci a duniya.
"Ina ganin yakin da ake yi da mu da kuma yakin da ake yi da al’adunmu na Yahudawa da Kiristoci, ana gwabza shi a ko’ina cikin duniya."
"Kuma ana yin wannan yaki ne musamman ta hanyar kungiyoyi biyu, masu sattsauran ra’ayin Shi’a da kuma masu tsattsauran ra’ayin Sunni.”
“Hakan na nufin wata tawaga da Iran ke jagoranta, wadda aka raunana kwarai amma har yanzu tana nan, da kuma tawagar Sunni da Muslim Brotherhood ke jagoranta, wadda ta bazu ko’ina.”
- Benjamin Netanyahu
Netanyahu ya yi zargi kan muzgunawa Kiristoci
Netanyahu ya ce waɗannan kungiyoyi suna shiga Turai, Amurka da Afirka, har da Najeriya, inda ya ce suna sane da cewa ana tsananta wa Kiristoci a sassa daban-daban na duniya.
“Muna sane da cewa ana tsananta wa Kiristoci a Gabas ta Tsakiya, a Siriya, a Lebanon, a Najeriya, a Turkiyya da sauran wurare."
"Mun san, kamar yadda ku ma kuka sani, cewa kasa guda ɗaya ce ke kare al’ummar Kiristoci, tana ba su damar bunkasa, tana kare su, tana tabbatar da cewa suna rayuwa lafiya kuma wannan kasa ita ce Isra’ila. Babu wata kasa daban. Babu."
- Benjamin Netanyahu
Wane shiri Israila ke yi?
Netanyahu ya ce Isra’ila na shiga wani yunkuri na haɗa kasashe masu goyon bayan al’ummomin Kiristoci a duniya, musamman waɗanda ke cikin mawuyacin hali kuma suka cancanci taimako.
“Yadda kuke taimaka mana, haka ma mu muna son taimaka muku. Kuma muna da ikon yin hakan. A Afirka, ta hanyar bayanan sirri, a Gabas ta Tsakiya, ta hanyoyi da dama da ba zan lissafo su ɗaya bayan ɗaya ba."
- Benjamin Netanyahu
Ya ce wannan ne babbar ajandar Isra’ila, kuma muhimmin ɓangare ne na manufofinta.

Source: Twitter
Netanyahu ya gana da Trump
Jawabin Netanyahu ya zo ne kwana guda bayan ganawarsa da shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya sanar da kai hare-haren sama a Najeriya a ranar Kirsimeti.
A ranar da aka kai hare-haren, Netanyahu ya ce dole a kawo karshen hare-haren da ake kai wa Kiristoci a Najeriya.
Isra’ila ita ce kasa guda tilo da ta fito fili ta mara wa Amurka baya kan ikirarin cewa ana tsananta wa Kiristoci a Najeriya.
Kasashen biyu dai abokan hulɗa ne na kud-da-kud a fannin siyasa da tsaro.
Israila ta yi kira ga 'yan Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jakadan Israila a Najeriya, Michael Freeman, ya aika sako na musamman ga 'yan Najeriya.
Michael Freeman ya yi kira ga 'yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya da juna ba tare da nuna bambanci ba.
Jakadan na Israila ya bukaci a zauna cikin fahimtar juna da girmama kowa, ba tare da la’akari da bambance-bambancen addini ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


