Wa'azin Wani Malami Ya Ratsa Zuciyar Shugaban Majaliasr Dattawan Najeriya, Akpabio
- Wa'azin wani malamin coci a jihar Akwa Ibom ya taba zuciyar shugaban majalisar dattawa ta Najeriya, Sanata Godswill Akpabio
- Sanata Akpabio ya umarci lauyoyinaa da su janye duk wata kara ya shigar gaban kotu kan wadanda suka bata masa suna
- Malamin cocin ya ja hankalin mabiyansa kan muhimmancin yafiya da nuna wa juna kauna a nasiharsa ta shiga sabuwar shekara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom, Nigeria - Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya umurci lauyoyinsa da su janye dukkan ƙorafe-ƙorafen ɓata suna da ya shigar a kotu.
Sanata Akpabio ya tabbatar da janye kararraki da ya shigar a kotu kan wasu mutane da yake zargi da yi masa ƙarya, kage da kuma bata masa suna.

Source: Facebook
Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a Cocin Sacred Heart Parish da ke Uyo, bayan sauraron wa'azin da limamin cocin ya gabatar, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Sanata Akpabio ya yafewa Natasha
Ko da yake bai ambaci sunaye ba, ana sa ran matakin zai shafi shari’ar da ya shigar kan Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan.
Shugaban Majalisar Dattawan ya bayyana cewa wa'azi da nasihar da malamin cocin ya gabatar sun ratsa zuciyarsa kuma ya yafe wa dukkan wadanda suka bata masa suna.
Ya ce hudubar da limamin cocin ya yi, wadda ta mayar da hankali kan afuwa, nuna ƙauna da yafiya ga makiya, ta taɓa zuciyarsa ƙwarai.
“Ina da kusan shari’o’i tara a kotu a kan wasu mutane da suka ɓata min suna, suka yi mini ƙarya, suka yi mini kazafi.
“Amma bayan sauraron wa'azin limamin mu, sai na ji kamar da ni yake kai tsaye Saboda haka, ina umartar lauyoyina da su janye dukkan shari’o’in da na shigar a kansu.”
Karar da Akapabio ya shigar da Natasha
A shekarar 2025, Akpabio ya kai ƙarar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT), bisa zargin ta yi masa ƙarya kan batun nemanta da lalata.
A ƙarar da lauyansa, S. I. Ameh, SAN, ya shigar a ranar 25 ga Agusta, Akpabio ya nemi diyyar Naira biliyan 200, tare da ƙarin Naira miliyan 500 na kuɗin shari’a.
Haka kuma, ya buƙaci Sanata Natasha ta fito ta ba shi hakuri sannan ya wallafa labarin a manyan jarudun kasar nan, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Source: Twitter
Wane wa'azi limamin cocin ya yi?
A cikin wa'azin da ya yi, limamin cocin Sacred Heart Parish, Rabaran Donatus Udoette, ya shawarci mabiya cocin da su rungumi zaman lafiya, yafiya da sulhu.
"Ku manta da abin da ya wuce duk radadinsa, dukkanmu muna ɗauke da nauyin raɗaɗi a zuciya. Don haka dole mu yafewa juna idan muna son ci gaba," in ji shi.
Wannan jan hankali ne ya ratsa zuciyar Akpabio, har ya umarci lauyoyinsa su janye duk wata kara da ya shigar a gaban kotu kan wadanda suka masa kage da karya.
Ana zargin wasu na shirin taige Akpabio
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar National Grassroots Movement (NGM) ta yi zargin an shirya wata makarkashiya da nufin tsige shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Kara karanta wannan
Akpabio: Kungiya ta bankado makarkashiyar da ake kullawa shugaban majalisar dattawa
Zargin na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya fito ya musanta rahotannin shirin tunbuke Akpabio.
Sai dai kungiyar ta yi zargin cewa wasu sanatocin Arewa sun tsara shiri sauke Akpabio, tana mai gargadin cewa su guji kawo abin da zai wargaza zaman lafiya a majalisar dattawa
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

