Ana Rade Radin Komawa APC, Mataimakin Gwamnan Kano Ya Tura Sako ga Abba da Kwankwaso
- Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ya fitar da sakon taya murnar shiga sabuwar shekarar miladiyya watau 2026
- A sakon da ya fitar duk da ya tafi Umrah Saudiyya, Aminu Gwarzo ya taya Gwamna Abba da jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso murna
- Ya kuma yi addu'ar Allah ya sa shekarar 2026 ta kasance mai zaman lafiya, hadin kai da ci gaban al'ummar jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf, jagoran NNPP na ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso, da al’umma murnar shiga sabuwar shekara ta 2026.
Wannan sakon taya murna na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin rikici da yiwuwar sauya sheƙar Gwamna Abba zuwa APC.

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa jam'iyyar NNPP a Kano da tafiyar Kwankwasiyya sun afka cikin rikicin cikin gida, inda kan mambobi ya fara rabuwa kan rade-radin shirin Gwamna Abba na komawa APC.

Kara karanta wannan
Ana rade radin zai koma APC, Gwamna Abba ya yi jawabi bayan sa hannu kan kasafin 2026
Rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka mataimakin gwamnan Kano na ƙasar Saudiyya domin gudanar da Umrah yayin da wannan lamari ke ci gaba da ɗaukar hankali a jihar.
Haka zalika ana rade-radin cewa Aminu Gwarzo na neman yi wa Abba bore, inda rahotanni ke cewa yana goyon bayan Sanata Kwankwaso.
Wane sako ya tura wa Abba da Kwankwaso?
A saƙon da kakakinsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar kuma Kwankwasiyya Reporters ta wallafa a Facebook, mataimakin gwamnan ya gode wa Allah bisa ni’imar rayuwa da damar ganin 2026 cikin koshin lafiya da cigaba.
Ya yaba wa Gwamna Abba kan abin da ya kira shugabanci mai hangen nesa, jajircewa wajen kula da jin daɗin al’umma, da kuma ƙoƙarin dawo da martaba da kima ta Jihar Kano ta hanyar manufofi da ayyukan raya kasa da suka shafi talakawa kai tsaye.
Haka kuma, Gwarzo ya jinjinawa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa rawar da yake takawa na jagoranci, ba da shawarwari na siyasa da kuma irin kulawar uba da yake yi.
Mataimakin gwamna ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin Abba na ƙarfafa kyakkyawan shugabanci, inganta ci gaban ƙananan hukumomi da tabbatar da adalci da daidaito a dukkan bangarori.

Source: Twitter
Mataimakin gwamna ya yi kira ga 'yan Kano
Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da zama masu bin doka da oda tare da mara wa gwamnati baya a ƙoƙarinta daga darajar jihar.
A ƙarshe, Gwarzo ya yi addu’ar Allah Ya sanya sabuwar shekarar ta kasance cike da zaman lafiya, haɗin kai, albarka da cigaba ga al’ummar Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Gwamna Abba ya sa hannu a kasafin 2026
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan dokar kasafin kudin 2026 a fadar gwamnatinsa da ke cikin birnin Kano.
Da yake jawabi bayan sa hannu, Gwamna Abba ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa gwamnatinsa za ta aiwatar da kasafin domin inganta rayuwar jama’a.
Ya bukaci mambobin majalisar zartarwarsa ta Kano da su ƙara ba gwamnati goyon baya tare da ƙwazo da jajircewa wajen aiwatar da manufofin ci gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
