An Sanya Ranar da Gwamnan Filato Zai Shiga Jam'iyyar APC bayan Ya Fice daga PDP
- Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya yi murabus daga jam’iyyar PDP, inda ya kammala shirye-shiryen komawa APC mai mulki a kasa
- Mutfwang ya ce komawa APC zai taimaka wajen hada kai da gwamnatin tarayya domin samar wa al'umma romon dimukuradiyya
- An sanya ranar da za a gudanar da taron mika wa gwamnan katin jam'iyyar APC a fadar gwamnati kafin ya gana da shugabannin jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya bayyana murabus dinsa daga jam’iyyar PDP, inda ya kammala shirye-shiryen komawa jam’iyyar APC a ranar Juma’a.
Mun ruwaito cewa matakin ya zo ne mako biyu bayan da shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya fara bayyana cewa gwamnan ya sauya sheƙa.

Source: Twitter
Gwamna Mutfwang ya fice daga PDP
Ko da yake an sami takaddama a baya kan wannan batu, wasiƙar murabus ɗin gwamnan ta kawo ƙarshen dukkan wani shakku, in ji rahoton Daily Trust.
A cikin wasiƙar murabus ɗinsa mai kwanan wata 29 ga Disamba, 2025, wadda ya aika wa shugaban mazaɓar Ampang ta Yamma da ke ƙaramar hukumar Mangu, Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa ya bar jam'iyyar ne nan take.
Ya bayyana cewa yanayin siyasar ne ya tilasta masa neman wani sabon dandamali domin ya ci gaba da yi wa al’umma hidima yadda ya kamata.
Ya kuma miƙa godiyarsa ga jam’iyyar PDP bisa damar da ta ba shi na takara a ƙarƙashin inuwarta har ma ya samu damar lashe zabe ya zamo gwamna.
Dalilan sauya sheƙar Gwamna Mutfwang
Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa komawarsa APC mataki ne na dabara wanda ya ɗauka domin amfanin al’ummar jihar Plateau baki ɗaya.
A cewarsa, wannan matakin zai taimaka wajen haɗa manufofin ci gaban jihar da na gwamnatin tarayya, wanda hakan zai kawo saurin bunƙasa tattalin arziki da kuma samar da romon dimuƙuradiyya ga jama’a.
Ya jaddada cewa babban burinsa shi ne samar da shugabanci na gari da kuma kawar da duk wani shinge na rarrabuwar kai a jihar, in ji rahoton jaridar The Sun.

Source: Twitter
Shirin karɓar Gwamna Mutfwang a APC
Darakta a fannin yaɗa labarai na gwamnan, Gyang Bere, ya tabbatar wa manema labarai cewa za a miƙa wa gwamnan katin zama memba na APC a ranar Juma’a a fadar gwamnati da ke Rayfield.
Bayan kammala rantsuwar, gwamnan zai wuce zuwa sakatariyar APC da ke Kalwa House domin ganawa da shugabannin jam’iyyar da magoya baya.
Bere ya yi kira ga dukkan magoya baya da abokan arziki da su fito su shaida wannan babban taron tarihi na sauya shekar Gwamna Mutfwang da za a gudanar.
An hallaka mutane a Filato
A wani labari, mun ruwaito cewa, manoma tara ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan wasu mahara sun kai farmaki kauyen Bum da ke Jos ta Kudu.
Harin ya faru ne duk da cewa an bayar da rahotannin sirri na harin, wanda ya yi sanadiyyar daidaita daukacin wani iyali a Bum.
Shugabannin yankin sun koka kan yadda jami'an tsaro suka kasa dakile harin da ya faru lokacin da mutane ke tsaka da barcin dare.
Asali: Legit.ng

